Yaro mai basira ya ƙera masallacin Makka da kwalaye a Maiduguri

Daga WAKILINMU

Wani haziƙin yaro mai shekaru 15 da haihuwa da ake kira Aji Bukar Haziki, ya haɗa makwafin babban masallacin Ka’aba sai, da kwalaye a garin Maiduguri, na Jihar Borno.

A cikin wani bidiyo wanda ya yi ta yawo a soshiyal midiya, za a ga yaron a tsaye a bayan masallacin da ya haɗa. 

Shi dai wannan babban masallacin na Makka ana kiransa da Masjid al-Haram, wato masallaci abin girmamawa. Shi ne masallacin da ya ke kewaye da Ka’aba a garin Makka ta ƙasar Saudiyya.

Shi ne kuma muhallin aikin Hajji da Umrah wanda addinin Musulunci ya umarci kowanne Musulmi ya gudanar aƙalla sau ɗaya a rayuwarsa.

Kuma ɗaya daga cikin abubuwan da suka wajaba a kan mahajjatan shi ne, zagaye Ka’aba wacce ta zama cikamakon aikin hajjin.

Haka zalika, akwai kuma Hajarul Aswad, fitar da Maƙam Ibrahim, da dutsen Safa da Marwa.

Masallacin Ka’aba an sha yi masa gyarraki da garambawul a tsahon shekarun da aka yi shi. 

Tuni dai masu kallon bidiyon fasihin yaron suka yi ta tofa albarkacin bakinsu a kan wannan aikin hikima da Aji Bukar ya yi.