Sin da Afirka na yin tasiri mai yaƙini a duniya

Daga BELLO WANG

Wasu abubuwa guda 2 da suka faru a kwanan baya sun nuna haɗin gwiwar ƙut da ƙut da ƙasashen Afirka da ƙasar Sin suke yi a fannin kula da harkokin ƙasa da ƙasa.

Ɗaya shi ne yadda Afirka da Sin suka haɗa kai wajen tabbatar da an zartas da ƙudurin kafa asusun biyan diya ga ƙasashe masu tasowa, wadanda suka samu hasara sakamakon bala’un da sauyawar yanayin duniya ke haddasawa, a taron ɓangarorin da suka sanya hannu kan yarjejeniyar tinkarar sauyawar yanayi ta MƊD na COP27, wanda ya kasance wata babbar nasarar da ƙasashe masu tasowa suka cimma a ƙoƙarinsu na muhawara da ƙasashe masu sukuni.

Ɗayan kuwa shi ne yadda ƙasar Sin ta nuna goyon baya ga ƙungiyar tarayyar ƙasashen Afirka ta AU kan batun halartarta ƙungiyar ƙasashe masu ƙarfin tattalin arziki ta G20, inda a wajen taron ƙolin G20 na 17 da ya kammala a kwanakin baya, ƙasar Sin ta zama mambar ƙungiyar G20 ta farko da ta nuna goyon baya ga ƙungiyar AU a fili.

Na san waɗannan abubuwa za su sanya ku yin tambayar cewa, mene ne ya sa har kullum ƙasashen Afirka da ƙasar Sin ke hadin kai da juna, yayin da suke kula da al’amuran ƙasa da ƙasa?

A gani na, dalili shi ne, ƙasar Sin da ƙasashen Afirka suna da tunani iri ɗaya.

Da farko, dukkansu na son tabbatar da yanayi na adalci a duniya.

Saboda sun taba shan wahala sakamakon tsare-tsaren duniya da ƙasashen yammacin duniya ke jagoranta, inda a kan yi musu danniya a fannonin siyasa da tattalin arziki.

Wannan niyyar bai ɗaya, ta zama wani tushe mai ƙarfi ga haɗin gwiwar Sin da Afirka.

Idan mun dauki maganar tinkarar sauyawar yanayin duniya a matsayin misali.

Ƙasashen yamma sun buƙaci ƙasashen Afirka da su ɗauki nauyin rage fitar da iska mai dumama yanayi iri ɗaya da nasu, ko da yake haƙiƙanin adadin iskar da ƙasashen Afirka ke fitarwa bai wuce kaso 3 bisa dari na jimillar adadin dukkanin duniya ba.

Sai dai a nata ɓangare, ƙasar Sin ta jaddada buƙatar ɗaukar nauyi mabanbanta tsakanin ƙasashe masu sukuni da masu tasowa.

Sa’an nan ƙasar Sin ita ma tana fuskantar matsin lambar da ƙasashen yamma suke yi mata, inda suke neman soke matsayin ƙasar na wata ƙasa mai tasowa, don dora mata matuƙar nauyi na rage fitar da hayaƙi da samar da kuɗi.

Duk da haka, ƙasashen Afirka sun yaba wa ƙasar Sin kan yadda take kokarin samar da gudunmowa ga aikin raya makamashi masu tsabta a duniya, kana sun buƙaci ƙasashen yamma da su ɗauki ƙarin nauyi, bisa yadda suka daɗe suna fitar da dimbin hayaƙi mai guba cikin shekaru 200 da suka wuce.

Na biyu shi ne, ƙasashen Afirka da ƙasar Sin suna ɗora matuƙar muhimmanci kan abu ɗaya, wato neman ci gaba.

Sabanin yadda wasu ƙasashen yamma suke dora muhimmanci kan kare ikonsu na yin babakere a duniya, da takara da wasu ƙasashe, Sin da Afirka na ta ƙoƙarin neman hanyar raya ƙasa.

Misali, a taron G20 na wannan karo, ƙasashen yamma sun fi mai da hankali kan batun ɗora wa ƙasar Rasha taken “kasa mai kai hari ga saura”, yayin da a nasu bangare, shugabannin ƙasashen Afirka da Sin ke nanata kalmomi irinsu “haɗin kai”, da “raya kasa”, da “amfanin kowa”, da dai sauransu, a cikin jawaban da suka gabatar.

Ya kamata mu tuna da cewa, yawan al’ummar ƙasar Sin da ta ƙasashen Afirka ya kai fiye da kashi 35% na ɗaukacin al’ummar duniya.

Duk waɗannan mutane masu yawa haka, suna son tabbatar da yanayin adalci a duniya, da ƙoƙarin haɗin gwiwa don kare moriyar kowa, wannan abun alheri ne ga ɗaukacin ‘yan Adam, wanda ke samar da tasiri mai yakini ga duniyarmu ta wannan zamani.

Mai fassara: Bello Wang