An yi ganawa tsakanin ministocin tsaron ƙasashen Sin da Amurka

Daga CMG HAUSA

Yau Talata, ministan tsaron ƙasar Sin Wei Fenghe wanda ke halartar taron ministocin tsaron ƙasashen ASEAN karo na 9 da ke gudana a Cambodiya, ya gana tare da takwaransa na ƙasar Amurka Lloyd Austin bisa gayyatar da ya yi masa.

Ɓangarorin biyu na ganin cewa, ya kamata sojojin ƙasashen biyu su yi ƙoƙarin tabbatar da matsaya ɗaya da shugabannin ƙasashen biyu suka cimma.

Yayin ganawar tasu, Wei Fenghe ya nanata matsayin Sin kan batun yankin Taiwan.

Ya ce, batun yankin Taiwan yana da muhimmanci ga muradun ƙasar Sin, da ma hulɗar ƙasashen biyu.

Taiwan wani yanki na ƙasar Sin, kuma batun yankin, harkokin cikin gida na ƙasar Sin ne, ba wanda ke da ikon tsoma baki a cikinsa.

Mai fassara: Amina Xu