Ronaldo ya zama mutum na farko da ya samu mabiya miliyan 500 a Instagram

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Ɗan wasan gaban Portugal, Cristiano Ronaldo ya zama mutum na farko da ya fara samun mabiya miliyan 500 a manhajar Instagram, miliyan 124 fiye da Lionel Messi, wanda ya zo na 2.

Shahararren ɗan wasan Manchester United ne mutane suka fi bibiyar a Instagram, kuma ya zama mutum na farko da ya haura mabiya miliyan 500 a shahararren dandalin sada zumuntar.

Ronaldo kuma shi ne gaba ɗaya wanda ya fi yawan mabiya a Instagram, da kuma a Facebook. Lionel Messi na biyu yana da mabiya sama da miliyan 376 a Instagram.