Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Wata mummunar gobara ta tashi a safiyar Laraba a Babbar Kasuwar Katsina, inda ta ƙone shaguna da dukiyoyi na daruruwan miliyoyin naira.
Shaidu sun bayyana cewa gobarar ta fara ne kafin wayewar gari, sannan ta bazu cikin sauri zuwa wasu sassan kasuwar, lamarin da ya sa ‘yan kasuwa suka kasa ceton hajojinsu yayin da wutar ke cinye shagunan da ke ɗauke da kayan abinci, yadudduka da sauran kayayyaki.
Da yawa daga cikin ‘yan kasuwar da suka isa kasuwar bayan samun kiran gaggawa sun tarar da ɓarnar da gobarar ta yi, inda suka ga hayaƙi mai kauri, ƙarafa da suka narke da kuma ragowar shagunan da suka ƙone.
ɗaya daga cikin waɗanda gobarar ta shafa, cikin hawaye, ya shaida wa Daily Trust cewa, ya rasa duk abin da ya kwashe shekaru yana ginawa cikin ‘yan mintuna kaɗan.
“Duk abin da na yi wa rayuwata aiki tsawon shekaru ya tafi. Wannan shago shi ne rayuwata. Ban san yadda zan fara ba,” inji shi.
Wani ɗan kasuwa kuma ya dora alhakin yawan barnar da aka yi kan jinkirin da jami’an kashe gobara suka yi kafin isa wurin.
“Kafin jami’an kashe gobara su iso, wutar ta riga ta lalata komai. Har yanzu ana neman mu bayar da kuɗin man fetur idan gobara ta tashi,” in ji shi.
Daga bisani jami’an Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Katsina sun isa wurin tare da shawo kan gobarar, amma ‘yan kasuwar sun ce jinkirin da aka samu ya bai wa wutar damar bazuwa zuwa shaguna da dama.
Shugabannin ƙungiyar ‘Yan Kasuwar Kasuwar Tsakiya ta Katsina sun bayyana lamarin a matsayin wani sabon tunatarwa kan matsalolin da ke addabar ayyukan gaggawa a jihar.
A cewarsu, sau da dama ‘yan kasuwa kan tara kuɗin man fetur kafin motocin kashe gobara su amsa kiran gaggawa.
ƙungiyar ta roƙi gwamnatin jihar da ta gaggauta ɗaukar matakan ƙarfafa hukumar kashe gobara.
“Muna roƙon gwamnati ta ƙarfafa hukumar kashe gobara. Gobara na buƙatar ɗaukar mataki cikin gaggawa, ba jinkiri saboda rashin mai ba,” in ji shugaban ƙungiyar.
Ya yi gargaɗin cewa matuƙar ba a samar wa hukumar isassun kuɗi da kayan aiki ba, irin wannan gobara za ta ci gaba da barazana ga rayuwar ‘yan kasuwa.
Wasu daga cikin ‘yan kasuwar sun nuna takaicinsu kan cewa da an kai ɗauki cikin lokaci, da an rage yawan asarar da aka yi.
“Da taimako ya zo da wuri, da gobarar ba ta bazu haka ba. Bai kamata a jira tara kuɗin mai ba kafin a kai ɗauki a lokacin gaggawa,” wani ɗan kasuwa ya ce.
Ko da yake babu wanda ya rasa ransa a gobarar, wani jami’in kashe gobara mai suna Idris Gachi ya samu mummunan rauni a ƙafarsa yayin ƙoƙarin kashe wutar.
Da yawa daga cikin waɗanda gobarar ta shafa sun ce yanzu rayuwar iyalansu ta shiga cikin rashin tabbas domin kasuwar ce kaɗai hanyar samun kuɗin shigarsu.
