Na yi nadamar yi wa Tinubu kamfe a 2023 — Ɗanbilki Kwamanda

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Fitaccen ɗan siyasa kuma jigo a Jam’iyyar APC a Jihar Kano, Abdulmajid ɗanbilki Kwamanda, ya ce ya yi nadamar mara wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu baya a zaɓen 2023.

Yayin da yake zantawa da manema labarai, Kwamanda ya ce Shugaba Tinubu ya watsar da waɗanda suka sha wuya a kansa, duba da halin da ƙasa ke ciki a yanzu.

Ya bayyana cewa, a duk tsawon rayuwarsa, bai taɓa yin nadamar wani abu kamar yadda ya yi nadamar mara wa Tinubu baya ba.

“Da ciwo, amma dole a faɗi gaskiya. Ni cikakken ɗan jam’iyyar APC ne, amma dole na amince cewa gwamnatin APC ta gaza a wajen ‘yan Nijeriya.

“Na sadaukar da lokaci da dukiyata wajen shawo kan mutane su zaɓi jam’iyyar, amma a yau ina nadamar hakan,” inji shi.

Kwamanda, ya kuma nemi afuwar jama’a, inda ya bayyana cewa abubuwan da ya musu alƙawari a kai za a musu, gwamnatin APC ba ta cika ba.

“’Yan Nijeriya na cikin yunwa kuma suna cikin fushi. Ba su da tabbas kan tsaro, kuma mulki ba ya tafiya daidai.

“Yawancin mutane ba sa iya cin abinci sau biyu a rana,” inji shi.

ɗanbilki Kwamanda ya yi ƙaurin suna wajen suka da yin adawa mai zafi a tsakanin abokan hamayyar jam’iyyarsa a Jihar Kano.

By ukarofi