Daga RABILU ABUBAKAR a Gombe
Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta ƙasa (NAFDAC) ta gargaɗi masu sayar da ‘ya’yan itatuwa a jihar Gombe kan hatsarin amfani da sinadarin Carbide wajen sanya ‘ya’yan itatuwa su nuna cikin gaggawa. Wannan mataki na daga cikin ƙoƙarinta na kare lafiyar al’umma daga illolin wannan mummunar ɗabi’a.
A yayin taron wayar da kai da aka gudanar a babban kasuwar Gombe, Shugaban NAFDAC na jihar, Mista James Agada, ya bayyana cewa amfani da sinadarin Carbide wajen sanya ‘ya’yan itatuwa su nuna da wuri yana da matuƙar hatsari ga lafiyar bil’adama.
“’Ya’yan itatuwa suna da muhimmanci wajen gina jiki, musamman a lokutan azumi, inda mutane ke amfani da su wajen bude baki. Amma, amfani da ‘ya’yan itatuwa da aka sanya suka nuna da sinarin carbide na iya haddasa cutar daji (cancer), matsalolin fata, da sauran munanan cututtuka,” inji Agada.
Ya yi kira ga masu sayar da ‘ya’yan itatuwa da su daina wannan dabi’a, yana mai jan hankali cewa NAFDAC tana da hurumin hukunta masu aikata irin wannan laifi. Duk da haka, ya ce a halin yanzu hukumar tana ƙoƙarin tattaunawa da masu ruwa da tsaki domin wayar da kai maimakon amfani da ƙarfi.
“Mun fi son ilmantarwa da tattaunawa da ku domin ku fahimci illar wannan ɗabi’a, kuma mu haɗa kai domin kawar da ita saboda amfanin kowa da kowa,” ya ƙara da cewa.
Wani jami’in NAFDAC, Mista Musa Haruna, ya jaddada cewa wannan matsalar ta Carbide ba ta taƙaita ga Gombe ko Nijeriya kaɗai ba, illa matsala ce ta duniya baki ɗaya.
Ya ce tare da haɗin kai daga masu sayar da ‘ya’yan itatuwa, za a iya kawar da wannan matsala.
“Wannan al’amari ya zama matsalar duniya gaba ɗaya. Amma tare da goyon bayanku, NAFDAC za ta tabbatar da kawar da shi a nan Gombe,” Haruna ya tabbatar.
A madadin masu sayar da ‘ya’yan itatuwa, Mataimakin Shugaban ƙungiyar, Abdullahi Bello Muhammad, ya yabawa kokarin NAFDAC kuma ya ce kungiyar ta fara daukar mataki tun bayan wata ganawa da shugabannin ƙaramar hukumar Gombe da Yeriman Gombe.
Ya ƙara da gargaɗi cewa duk memban da aka samu yana amfani da carbide zai fuskanci hukunci mai tsauri, wanda zai iya kaiwa ga dakatarwa daga ƙungiyar.
Daga ƙarshe, wasu daga cikin mambobin kungiyar sun yi alƙawarin yaɗa wannan saƙo ga abokan aikinsu tare da tabbatar da cewa babu wanda zai karya wannan doka. Sun tabbatar da cewa za su sanya ido sosai domin ladabtar da duk wanda ya ci gaba da amfani da carbide wajen sanya ‘ya’yan itatuwa su nuna da wuri.
Wannan gargaɗi na daga cikin matakan NAFDAC na tabbatar da ingancin abinci da kare lafiyar al’umma a Nijeriya.
