Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Mataimakin Shugaban ƙasa, Kashim Shettima, ya yi kira ga shugabannin majalisun Nijeriya da su cigaba da ƙoƙarin sauke nauyin da ya rataya a wuyansu tare da bai wa haɗin kai da cigaban ƙasa muhimmanci sama da bambance-bamnbance na siyasa.
Ya bayyana hakan ne a ranar Litinin da daddare a lokacin da Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya gayyaci shugabannin majalisar wakilan liyafar buɗa baki na Azumin watan Ramadan a ɗakin taro na da ke fadar shugaban ƙasar a Abuja.
A yayin da yake magana a madadin shugaban ƙasa, Shettima ya buƙaci ‘yan majalisar da su kula da nauyin da ke kansu cikin ƙanƙan da kai da kuma jajircewa wajen samar da cigaba.
Ya ce, “a ƙarshe, wajen yi mana alƙalanci, tarihin ba zai yi la’akari da irin faɗace-faɗacen da muke yi a tsakanin ba, zai kalli irin ayyukan da muka haɗu muka yi ne bakiɗaya. A yau an gayyace ku ne zuwa nan ba don kasancewarmu maƙiya ba, sai don kasancewarmu abokan aiki wajen gina ƙasar nan.
“A wannan wata mai albarka, ya kamata mu yi amfani da shi wajen samar da zaman lafiya a maimakon rikici, haɗin kai a maimakon faɗa, tattaunawa da maimakon kace-na-ce. Abin da ya haɗa mu guri guda ya fi bambancin da muke da shi a matsayin ƙasa guda ɗaya,” ya bayyana.
Sannan Shettima ya yaba wa irin jagorancin Shugaba Tinubu yana mai bayyana shi a matsayin shugaba mai hangen nesa da jawo kowa a jiki.
A cewar Shettima, “Shugaba Tinubu ba wai shugaba ne da za su yarda da shi ba, shi shugaba ne da shi ya yarda da su. Ya ɗauke ku ne a matsayin ginshiƙai na dimokraɗiyya, muryar jama’a, kuma abokan tafiya a wajen cikar burinmu na gina Nijeriya.”
Sannan ya ba wa ‘yan Nijeriya tabbacin cewa ana samun kyakkyawan sakamako na irin tsare-tsaren da shugaba Tinubu ke kawowa wajen farfaɗo da tattalin arziƙi da kuma ɗorewarsa.
“Za mu samar da Nijeriya da kowa zai yi cimma gaci da yin nasarar,” inji Shettima.
“Ba yadda za a samu cigaba ba tare da zaman lafiya ba kuma ba za a samu zaman lafiya ba idan ba cigaba. Haɗin kan da ake da shi a majalisar wakilai ‘yar manuniya ce na irin yadda muka ƙuduri aniyar samar da cigaba a Nijeriya.
Shettima ya buƙaci shugabanni da su ƙarfa shugabancinsu da nuna tausayi da adalci saboda su amintattu ne ga ‘yan Nijeriya.
“Shugabanci ba abu ne na cimma muradin ƙashin kai ba, abu ne na bauta wa al’umma. Nauyi ne aka ɗora mana da tarihi zai yi mana alƙalanci da irin yadda muka bai wa al’umma gudunmowa.”
Tun da fari, shugaban majalisar wakilai, Tajudeen Abbas, ya gode wa shugaban Tinubu kan gayyatarsu shan ruwa da ya yi da yadda yake girmama da nuna damuwa ga majalisar.
“Kamar yadda kuka sani, watan Ramadan ya ƙunshi abubuwa da yawa da suka haɗa da koma zuwa ga ubangiji da nazarin a ina kake da, ina kake yanzu, ina kake son zuwa gobe? Ina da tabbacin yanzu ne Nijeriya ta fi buƙatar irin wanann nazarin sama da kowanne lokaci,” ya faɗa.
Ya roƙi Musulmai da Kiristoci da da su riƙa yi wa kasar nan addu’a. Ya ce ‘yan Nijeriya sun san irin abin da Tinubu ya cimma a shekaru biyun da ya yi. Don haka lokaci ga kowa ya yi nazari da addu’a ga Nijeriya. Addu’a ga tattalin arziƙi da tsaro da addu’a ga shugabanni da al’umma bakiɗaya.
Ya kuma ba da tabbacin cewa dukkan ɗan majalisar yana goyon bayan Tinubu saboda tsare-tsarensa na inganta rayuwar al’ummar ƙasar nan.
A madadin ‘yan majalisar wakilai, muna ba da gudunmuwar Naira miliyan 705,000,000 da aka tattara daga kaso 50 na kuɗin albashi na ‘yan majalisar domin ayyukan jinƙai da Shugaba Tinubu ke yi da kuma tallafa wa marasa ƙarfi a Nijeriya.
