
Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI
A ranar Litinin 5 ga watan Agusta ne Naira ta samu farfaɗowa akan Dala da kaso 0.6 a kasuwar sunku inda a ke sayar da ita a N1,607.15.
Wata sanarwa daga FMDQ wanda zaure ne da ke kula da canjin kuɗin Nijeriya a kasuwannin duniya na NAFEM ya ce, Naira ta samu ribar N9.93 wanda ke wakiltar kaso 0.6 idan an kwatanta da darajarta ta ranar 2 ga watan Agusta da ke matakin N1,617.08 kowace Dala ɗaya.
Sakamakon haka, an samu raguwar adadin a ke fita a kullum daga Dala miliyan 131.55 zuwa Dala miliyan 77.09 daga ranar 2 ga watan Agusta.
Haka nan, matakin sanya hannun jari da kuma fitar da su, a na hada-hadar Nairar ne a tsakanin N1,620.50 da kuma N1,570.00 ga wane Dala.
