Nan ba da jimawa ba safarar ɗan-adam za ta zama tarihi – Gidauniyar FIAP yayin ganawar wakilan Sifaniya da Nijeriya

Spread the love

Gidauniyar Ƙasa da Ƙasa ta Bunƙasa Harkokin Gudanar da Ayyukan Gwamnati (FIAP) ta bayyana cewa, ana sa ran masu safarar mutane da masu fasa-ƙwaurin baƙin haure za su fuskanci tsauraran matakan jami’an tsaron haɗin gwiwa.

FIAP ta faɗi haka ne bayan kammala wani taron horaswa na kwanaki huɗu da aka shirya domin ƙarfafa binciken laifukan ƙetare iyakokin ƙasashe da suka shafi Safarar Mutane (TIP) da Fasa-ƙwaurin Bakin Haure (SOM).

Javier Leon, Mataimakin Shugaban Tawaga a FIAP kuma Babban Sufeto na Rundunar ‘Yan Sandan Ƙasar Sifaniya, ya ce mahalarta taron sun kammala horaswar mai zurfi ne da ƙarin ƙwarewa kan sabbin dabarun bincike da tsare-tsaren gudanar da ayyuka domin tunkarar ƙungiyoyin safarar mutane da fasakwaurin baƙin haure da ke ƙara amfani da dabaru masu sarƙaƙiya, tare da tabbatar da cewa an bai wa waɗanda abin ya shafa muhimmanci a duk matakan bincike.

Ya gargaɗi mahalarta da kada su bari sabbin dabarun da suka koya su wuce gona da iri wajen gudanar da bincike.

Haka kuma, ya jaddada cewa dole ne waɗanda abin ya shafa su kasance a matsayin ginshiƙin kowace rundunar bincike, kuma bai kamata a sake jefa su cikin wata cutarwa ko wahala ba a yayin neman tabbatar da adalci.

Leon ya bayyana taron a matsayin wata dama ta ɗaukar salon dabarun juna, inda ya ce ƙwararrun Sifaniya su ma sun samu muhimman darussa daga gogewa da ƙwarewar da jami’an binciken Nijeriya suka raba da su.

A cewarsa, musayar ilimi da ƙwarewa ta ƙara ƙarfafa amincewa tsakanin ƙasashen biyu, tare da samar da sabbin damarmaki na inganta dabarun bincike da zurfafa haɗin-gwiwar ayyukan yaƙi da manyan laifukan ƙungiyoyi masu tsallake iyakokin ƙasashe.

Babbar jami’ar ayyuka ta FIAP, Cayetana Bellisco, ta ce ɗaya daga cikin muhimman sakamakon taron shi ne ƙara bayyana buƙatar kafa rundunar bincike ta haɗin gwiwa tsakanin Nijeriya da Sifaniya domin yaƙi da manyan laifukan ƙungiyoyi, musamman safarar mata da yara.

Ta ce, irin wannan haɗin-gwiwa zai ƙarfafa musayar bayanan sirri, gudanar da bincike na haɗin-gwiwa da kuma matakan tabbatar da doka a ƙetare iyakokin ƙasashe domin tunkarar ƙungiyoyin masu aikata laifuka na ƙasa da ƙasa.

“Daga ɓangaren FIAP, mun ƙuduri aniyar ci gaba da wannan aiki ba tare da ja da baya ba,” in ji Bellisco.

Shi ma da yake magana, Mai Bada Shawara akkan Binciken Laifuka na FIAP, Sani Dantuni, ya bayyana horon a matsayin wani babban ci-gaba ga hukumomin da ke kan gaba wajen yaƙi da safarar mutane.

Ya ce, mahalarta sun samu ƙwarewar aiki a fannoni da suka haɗa da taimakon shari’a tsakanin ƙasashe, binciken laifukan kuɗi, tattara bayanan sirri daga kafofin buɗe ido, da kuma dabarun tarwatsa ƙungiyoyin masu aikata manyan laifuka.

A cewar Dantuni, mahalartan—waɗanda suka fito daga hukumomin da ke jagorantar yaƙi da safarar mutane a Nijeriya —yanzu sun fi samun ƙwarewa wajen binciken manyan laifukan ƙetare iyakokin ƙasashe da kuma ƙarfafa haɗin gwiwa ba kawai da Sifaniya ba, har ma da sauran ƙasashen Turai.

An shirya taron ne a ƙarƙashin Sashe na Uku na Shirin Tallafa wa Gudanar da Harkokin Fasa-Kauri a Nijeriya, wanda Tarayyar Turai ke ɗaukar nauyi.

Taron ya haɗa jami’ai daga Hukumar Yaƙi da Safarar Mutane ta Ƙasa (NAPTIP), Hukumar Kwastam ta Nijeriya, Hukumar Tsaro da Kare Fararen Hula ta (NSCDC), da Rundunar ‘Yan Sandan Nijeriya.

CSP Joy Abuma, jami’ar ‘yan sanda da aka tura aiki zuwa NAPTIP, ta ce taron ya sauya mata gaba ɗaya yadda take gudanar da binciken shari’o’in safarar mutane.

“Na shiga NAPTIP ne kwanan nan, kuma wannan horaswar ta buɗe min ido kan dabarun bincike da dama,” in ji ta.

Ta tuna da wani shari’ar safarar mutane da ta gudanar, inda ta rubuta sunan wanda abin ya shafa ba tare da sanin cewa hakan na iya ƙara jefa mutumin cikin haɗari ba.

“Kwanan nan na gudanar da wani bincike inda na rubuta sunan wanda abin ya shafa,” in ji Abuma. “Ta hanyar wannan horaswar, na koyi cewa dole ne a kare sirrin wanda abin ya shafa. Wannan ilimin zai taimaka mana wajen kare waɗanda abin ya shafa yadda ya kamata, gina amincewarsu da mu, da kuma ƙarfafa gurfanar da masu laifi a gaban kotu a nan gaba.”

By Babaji

Leave a Reply