Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Mashawarci na musamman kan dabarun yaɗa labarai ga shugaban ƙasa Bola Tinubu, Bayo Onanuga, ya ce nan ba da daɗewa ba ‘yan Nijeriya za su samu sauƙin rayuwa, yayin da sauye-sauyen tattalin arziki na gwamnati ke ƙara kunno kai.
Da yake magana da manema labarai a Legas ranar Lahadi, Onanuga ya bayyana cewa nan ba da daɗewa ba za a ga tasirin manufofin Tinubu a dukkan sassan ƙasar nan.
Onanuga ya bayyana cewa, ba wai kawai shugaban ƙasar ya gabatar da sauye-sauye na ci gaba bane, har ma ya magance ƙalubalen da gwamnatocin baya suka kaucewa.
Ya ƙara da cewa, shekaru biyu ba za su isa a auna cikakken nasarorin da gwamnati ta samu ba, yana mai cewa ƙwararru kan harkokin siyasa kan tantance tasirin manufofin ne cikin shekaru 10 zuwa 12.
“Shekaru biyu na Shugaban ƙasa na kan karagar mulki sun fara ne da aiwatar da wasu manyan manufofi.
“An gudanar da gyare-gyare da yawa a sassa daban-daban. Shugaban ƙasar ya shimfiɗa abubuwa da yawa da za su tabbatar da ci gaba,” inji shi.
Ya amince da cewa, yayin da kyawawan ayyukan shugaban ƙasa a cikin shekaru biyu da suka gabata ke kawo ci gaba sannu a hankali, an samu gagarumin sauyi a tattalin arzikin ƙasar, tare da magance matsaloli da dama.
Onanuga, yayin da yake magana kan halin da ake ciki kafin a cire tallafin, ya ce, “Babu mai, yawancin tashoshi suna cewa babu mai, babu mai.
“Abin da ke faruwa a wancan lokacin shi ne, NNPC ya kai ga gaci, bai da kuɗin shigo da mai, ta yi ikirarin cewa yana bin dillalai dala biliyan shida, kuma gwamnati na bin sa kusan dala tiriliyan huɗu, don haka ba zai iya shigo da shi ba.
Da yake magana game da lamuni, Onanuga ya fayyace cewa al’ada ce ta gama-gari a duniya, tare da ma ƙasashe irin su Amurka suna shiga ciki.
“Nijeriya na da albarkatu masu yawa da muke amfani da su, amma ba kuɗin da za a iya samu ba kamar yadda mutane ke zato,” inji shi.
Ya jaddada cewa ba a ɓarnatar da kuɗaɗen da aka karɓo ba, sai dai a yi amfani da su ne domin biyan buƙatun ƙasa.
