Yawaitar ’yan gwangwan da mabarata barazana ce ga tsaron Abuja – Wike

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Ministan Babban Birnin Tarayya, Abuja, Nyesom Wike, ya shaida wa babbar kotun tarayya da ke Abuja cewa ƙaruwar ’yan gwangwan, mabarata da masu kwana a waje a babban birnin na haifar da babbar barazana ga tsaro ga mazauna birnin.

Wike, a cikin wata takarda da ya shigar na adawa da ƙarar da aka shigar a madadin wasu marasa galihu mazauna babban birnin tarayya Abuja, ya shaida wa mai shari’a James Omotosho da ya yi watsi da ƙarar Naira Miliyan 500 gaba ɗayanta.

Ministan, wanda ya bayyana hakan a cikin takardar shaidar da Saidu Abdulkadir, wani Jami’in Sakatariyar Ayyukan Shari’a na Hukumar Babban Birnin Tarayya (Abuja) ya gabatar, ya ce bara ba sana’a ce da doka ta yarda da ita.

NAN ta ruwaito cewa, mazauna unguwar ta bakin wani lauya, Abba Hikima, sun kai ƙarar Wike da Sufeto Janar na ’yan sanda a matsayin masu amsa na 1 da na 2, inda suka buƙaci a biya su diyyar Naira Miliyan 500 bisa zargin tauye musu haƙƙi.

Hikima, wacce ita ce mai gabatar da ƙara, ta haɗa Darakta-Janar na Sashen Ayyuka na Jiha (DSS) da Hukumar Tsaro da Cibil Difens (NSCDC) da Babban Lauyan Tarayya (AGF) da Gwamnatin Tarayyar Nijeriya a matsayin masu amsa na 3 zuwa 6.

Ministan ya ce, an sha kama ‘yan gwangwan su na ɓarnatar da dukiyoyin jama’a kuma a mafi yawan lokuta suna zama ‘yan leƙen asiri ga masu garkuwa da mutane, masu haɗa kai da ƙungiyoyin ta’addanci.

Baya ga haka, Wike ya bayyana cewa, ƙaruwar mutanen maau kwana a ƙarƙashin gadoji a cikin babban birnin tarayya Abuja, ba tare da amincewar sa ba, ya saɓa wa dokokin ci gaba na Abuja, kuma yana da barazanar tsaro ga rayuka da dukiyoyin sauran mazauna birnin.

Ya ce ya saɓa wa dokar AEPB na shekarar 1997 da ta hana wani mutum ya yi fitsari ko bayan gida a waje, wanda hakan ya kuma saɓa wa tsarin Abuja.

“An Abuja ne tare da tanadi ga kowane ɓangare na tattalin arziki.

“Akwai tanadin wuraren zama, wuraren kasuwanci, wuraren addini da kasuwanni da dai sauran su.

“Saboda haka, sayar da kaya a titunan Abuja ban da kasuwar da aka ware ko kuma tsarin kasuwanci ya saɓa wa tsarin babban birnin tarayya Abuja da kuma dokar AEPB ta 1997,” inji shi.

A cewarsa, yawaitar mabarata da ɓarayin tituna da ke cikin babban birnin tarayya Abuja, yana zubar da mutuncin birnin, sannan kuma yana haifar da babbar barazana ga tsaro.

Ministan ya ce, yana da alhakin aiwatar da dokar kare muhalli ta tarayya, da kuma magance buƙatun jin daɗjn jama’a na mazauna babban birnin 

Ya ce, bisa ga dokokin da suka dace, an kafa Sakatariyar Ci gaban Jama’a (SDS) na FCTA a shekara ta 2004 don inganta rayuwar mazauna babban birnin tarayya Abuja da kuma kare haƙƙin masu rauni, gajiyayyu, tsofaffi da marasa galihu.

Ya ce, bisa la’akari da abubuwan da suka gabata, an kafa cibiyar koyar da sana’o’in hannu ta FCT da ke Bwari domin horar da waɗannan marasa galihu da sana’o’i domin su dogara da kansu.

Ya ce waɗanda ke cikin marasa galihu da suka ƙi shiga cikin shirye-shiryen koyon sana’o’i daban-daban na barazana ga tsaro, lafiya da kuma muhalli ga lafiyar masu ababen hawa, masu wucewa, rayuka da dukiyoyin jama’a.

Wike ya musanta keta haƙƙin masu rauni ko kuma tauye su a cikin birnin.

A cewarsa, babu wata shaida da ke nuna irin wannan cin zarafi a gaban kotu.

By ukarofi