NANS ta ba wa MultiChoice wa’adin kwanaki 7 don cire ƙarin farashin satalayi

Daga AMINA YUSUF ALI

Ƙungiyar ɗalibai ta ƙasa (NANS) yankin Kudu maso yammacin ƙasar nan, ta ba wa kamfanin satalayi na MultiChoice Nigeria, wa’adin kwanaki 7 kacal a kan ya soke ƙarin farashin da ya yi nufin yi a kan biyan tashoshin DSTV da GOTV.

Hakazalika ƙungiyar ta yi barazanar rufe dukkan wuraren da ake sayar da tauraron ɗan’adam ɗin na Multichoice.

Ƙungiyar ɗaliban ta bayyana haka ne a ranar Talatar da ta gabata a wani jawabi da shugaban tsare-tsarenta, Adejuwon Olatunji, da mataimakinsa, Alao John, da jami’inta na hulxa da jama’a, Opeoluwa Awoyinfa suka sanya wa hannu.

A kwanankin nan ne dai kamfanin satalayi na MultiChoice ya ba da sanarwar yin ƙari a kan farashin sabunta biyan kuɗi na tashoshin DST da GOTV da kaso 17 a wani sakon tes da suka aike wa da masu amfani da shi. Inda a saƙon suka ce sabon farashin zai fara aiki ranar Litinin 1 ga watan Mayu, 2023.

Kamfanin ya bayyana dalilinsa na ƙarin farashin da yadda al’amuran gudanarwar suka yi tsada.

Da suke nuna ƙin jininsu ga wannan hukunci na ƙarin farashi, NANS ta bayyana cewa, kamfanin na Afirka ta Kudu yana nema ƙuntata ‘yan Nijeriya da sa su a ƙunci ba tare da duba da yanayin matsin rayuwar da suke ciki ba.

NANS sun ƙara da cewa, duba da yadda ‘yan Nijeriya sun mamaye kaso 45 na masu amfani da DSTV a faɗin duniya, suna kira ga shugaban ƙasa Manjo Janar Muhammadu Buhari (mai ritaya), da ministan sadarwa da su amshe damar MultiChoice kuma su maye gurbinsa da wani zavin da ya dace. Domin a daina cutar ‘yan Nijeriya a kowanne lokaci.

A cewar NANS indai MultiChoice ba ta koma tsarinta na farko ba, har wa’adin kwanaki 7 ɗin suka cika, ta za su zama ba su da wani zavi illa su rufe dukka ofisoshin kamfanin har sai an biya musu buƙatunsu, wanda a cewar su, suna magana ne da yawun dukkan mutanen Nijeriya.