Matsalolin haƙora da yadda za a magance su (3)

Daga AISHA ASA

Mai karatu sannunka da jimirin bibiyar jaridar al’umma, Manhaja. Kamar yadda muka faro wannan darasi na matsalolin haƙora sati biyu baya, yau ma za mu kawo wasu daga matsalolin da yadda za a iya magance su. Idan kun shirya, zan ce Allah Ya sa a amfana da abinda za a karanta.

A wasu lokuta rashin hasken haƙora kan zama matsala ga mai tare da shi, saboda sau da yawa idan aka kalli haƙoran sai a yi wa mai su kallon ƙazami, duk da cewa, yana wanke su yadda ya kamata.

Sau da yawa akan bazama neman man wanke baki da ya dace da haƙoran, a namu tunanin rashin dace da man baki na ƙwarai ne ya janyo hakan. Sai dai abinda ba mu sani ba, wannan matsala ce da ke buƙatar a magance ta kamar kowacce, kafin a ga haƙoran a yanayin da ake buƙata.

Kuma za a iya amfani da busashen furen tumfafiya tare da alif (kaɗan sosai), sai a yi amfani da asuwaki, ana dangwalawa, ana gurje haƙoran sosai da shi. Sannan a bada minti ɗaya zuwa uku kafin a wanke bakin, amma ba tare da an haɗe wani abu daga cikin haɗin ba.

A ɓangare ɗaya, akwai disashewar haƙora da ke samuwa ta sandin yawan cin goro, ko shan taba sigari ko ta gari. Waɗannan kan kai haƙora ga tabo baƙi da ka vata haskensu. Wannan matsala na da bambanci da wadda muka yi magana kanta a sama.

Ita wannan za a fara da tsagaitawa ko daina amfani da abinda ke haddasa matsalar kafin a nemi lemun tsami a haɗa da furen tumfafiya a dafa sosai, sai a dinga kuskure bakin da su idan sun ɗan rage zafi, sai a bi baya da buroshi a darje haƙoran.