Shawara ga gwamnati kan kwashe ’yan Nijeriya daga Sudan zuwa Masar

Game da yadda na ke bibiyar batun ’yan Nijeriya da ke Sudan inda yaqi ya goce, a ganina akwai sarqaqiya musamman ganin wannan Talatar za a fara kwashe su zuwa Masar daga Khartoum yayin da wasu xalibai sama da mutane dubu sun shiga motacin bas suna ka iyaka da Ethiopia yadda suke Neman haurawa zuwa Addis Ababa, sun fara Shan wahala.

Gaskiya wancan hanya ta qasa cikin Ethiopia ba kyau akwai qarancin abinci da ’yan ta’adda a hanya, idan ba Allah ya kiyaye ba komai na iya faruwa don haka a bi a yi hattara. Ya kamata kafin a fara wannan tafiya a hango hatsarin da za a samu game da  yankewar abinci ko man mota ko lalacewar mota a hanya da rashin kyan hanya da hayaniyar soja a hanya sabo sun rabu kowace qungiya da wanda su ke bi. Matuqar akwai hatsari rashin fara tafiyar shi yafi Alheri. Nasan Sudan ta qasa sosai tun daga Yamma qasar Chadi har Eljinaina a Sudan zuwa Port Sudan Bahar Maliya ta gabas tafiya a qasar na da wahala a kwanciyar hankali balle lokacin yaqi. Naje aikin Hajj ta Mota bayan haka na shiga Sudan ta qasa aikin Jarida lokacin yaqin Darfur lamarin ba sauqi. Don na kwana takwas a Sahara bani da abinci sai gurasa da mangwaro da tumatir sau xaya na yi wanka a kwanakin. Qoqarin da za su yi shi ne haxa su wuri guda a nema musu abinci da ruwan sha a fitar da su zuwa wani gari da ba a faxa kafin a kwashe su. Hanya Mafi sauqi a kwashe mutanen zuwa Bahar maliya Port Sudan kamar yadda qasashen Turai da Larabawa ke bi wajen kwashe mutanen su ta jirgin ruwa zuwa Masar ko Jeddah sai a kwashe su a jirgin sama. 

Shawara ta biyu Kuma a fita da su daga Khartoum zuwa Kassala wakilan diflomasiyyar Nijeriya daga Eriteria su zo su shiga da su Asmara wanda tafiya ce da ba ta wuce kilomita dubu daya ba daga Eriteria sai a kwashe su a jirgin ruwa zuwa Legas ko jirgin sama zuwa Nijeriya. Da fatan Allah ya taimaka Ya sa a zauna lafiya.

Daga MUAZU HARDAWA, Editan Jaridar Alheri kuma Reporter Dandalkura Radio Bauchi. 08062333065.