Maza, sai mun gyara kanmu za mu samu mace tagari

Manhaja logo

Assalam alaikum. Fatan kowa yana lafiya, fatan kuma mun sallah lafiya. Allah Ya sa muna da rabon ganin da yawa a gaba.

Da yawan daga cikin maza na ganin mata a matsayin wata halitta mai murɗaɗɗen hali wacce da wuya ka gane ina ta dosa. Hakan na cima matan tuwo a ƙwarya kwarai. Mujallar Hivisasa ta ƙasar Kenya ta gudanar da bincike a kan musabbabin hakan. Kaɗan daga ciki binciken da suka gudanar sun gano cewa hormones ɗin mata na taimakawa wajen halayyarsu, hakan ya sa ake ganin mata masu wuyar sha’ani. Cikin mata kashi ɗari, kaso saba’in da biyar na amfani da zuciyarsu ne wajen aiwatar da harkokin rayuwarsu. Shi ya sa abu kaɗan kan iya hargitsa masu tunani fiye da maza.

Kowace mace na burin ganin ina ma mijinta ko saurayinta ya san wasu ababe da ta ke son ya sani game da ita da kuma ɗabi’arta ta mace. Ita mace ba kamar mota bace da ke zuwa da dokoki ko ƙa’idoji na yadda za a sarrafa ta. Da yawan maza na samun saɓanin ra’ayi da matan da suke so, babban matsalar a nan ita ce ta rashin sanin takamaimai me matan ke so.

Zan jero kaɗan daga cikin siffofin maza da mata ke fatan ina ma mazajensu na da su.

  1. Namiji mai jajircewa:

Kamar yadda na faɗa a farko cewa mata na amfani da zuciyarsu ne wajen aiwatar da harkokin rayuwarsu hakane. Misali za ka ɓata wa mace rai, a lokacin za ta yi amfani da zuciyarta ne wajen yanke ma hukunci. Tana iya cema ku rabu, amma hakan ba yana nufin da gaske ta ke ba.

Tana son ka zama mai kafiya a lokacin, maimakon ka ce ma ta ku rabun sai ka jajirce ka nuna kai a lokacin ma ka fara sonta. Ka ba ta duk wata kulawa da ta ke buƙata, kafin ka ce “me” za ta sakko. Saboda ta yi hakan ne dama don ta san shin har lokacin kana sonta ko a’a.

  1. Namiji mai sauraro:

Yana daga cikin halittar mata yawan surutu, saboda hakan ne mace ke son namijin da zai zama kamar aboki a wajenta yadda ta ke surutu da ƙawayenta. Burin mace shine a duk lokacin da ta ke magana, ka saurare ta, koda kuwa maganar ba ta da wani amfani a gare ta.

Tana son namijin da zai ce ma ta “a duk lokacin da kike buƙatar magana ina tare da ke”, ko wanda zai ce, “a shirye na ke idan kina buƙatar wani abu ki kira ni”. Hakan na nuna ma ta cewa kai mai sauraro ne, tabbaci haqiqa duk wata damuwarta ba za ta voye ma ba, saboda ka ba ta kunnuwarka. Tabbas, mata a duk inda suke su na son a saurare su, saboda sun ɗauki magana a matsayin babbar waraka ta damuwarsu. Misali mace idan tana cikin damuwa babban abin da ta ke so shine wa zata faɗa ma cikinta koda kuwa ba za ka magance ma ta ba, wannan faɗin da ta yi ya rage wani kaso daga cikin damuwarta.

  1. Isashshen namiji:

A duk inda mace ta ke tana son ta nunawa duniya cewa wannan ne mijinta ko saurayinta. Tana alfahari da cewa namijin da ta ke so ya isa. Abin nufi a nan ya zama gwarzo a fannin shi, misali idan shi Malamin makaranta ne, babban burinta a ce babu Malami kamar shi. A ko ina ta ke za ta bugi ƙirji cewa wannan mijinta ne.

  1. Namiji mai tsafta:

Mace na son gayu da ƙyal-ƙyali saboda suna matuƙar saurin ɗaukar hankalinta, ko a ina mace ta ke tana son ƙyal-ƙyali. Mafi yawan mata basu son namiji ƙazami.

Na taba hira da wata matashiya ta ke faɗa min cewa abu na farko da ta ke fara kallo a wurin duk namijin da ya tunkare ta shine ƙafarsa. Idan ta ga ƙafar da datti, an tara farce, ga faso ko qauje, to ta san ƙazami ne.

Kowace mace na da abin da ta ke so ga namiji. Burin kowace ɗin dai ta ga namiji fes-fes ya sha gayu. ko da kuwa ba su da tsada, matuƙar namiji ya san yadda zai ɗauko wanka zai birge mace.

  1. Namiji ya san me ke saurin sanya mace farin ciki da baƙin ciki:

Mata na da rauni saboda haka ne abu kazan ke saurin raunana musu zuciya. Bature ya ce, “Women are sensitive creatures”. Abin da zai samu farin ciki sai ya zama namiji na ganin ba wani abu bane ba, a wajen mace kuwa abu ne babba. Misali mace ta yi kwalliya tana son a yaba wannan kwalliyarta ta, amma da zarar ka yi kamar ba ka san ta yi ba, zai baƙanta ma ta rai.

Ka furta cewa, “My love, kin yi kyau fa sosai, kai har ma ka ƙara da cewa, kin fi kowaceace kyau a duniya”, farin cikin da zai sa ta ba kaɗan ba ne, sannan kai ma za ka ɗanɗana cikin farin cikin. A duk lokacin da ka faranta wa mace babban burinta a lokacin me za ta yi ta kyautata maka.

Wasiƙa daga MUSTAPHA MUSA, 08168716583.