Sudan: Jihohin Jigawa, Kaduna, Borno sun kwashe ‘ya’yansu zuwa gida daga Masar

Daga BASHIR ISAH

Da alama wasu daga jihohin Nijeriya sun ɗauki nauyin kwashe ‘ya’yansu da suka maƙale a Sudan zuwa gida bayan da Gwamnatin Tarayya ta yi jigilarsu zuwa ƙasar Masar.

Jaridar News Point Nigeria ta kalato cewar, jihohin da lamarin ya shafa sun haɗa da Borno da Jigawa da kuma Kaduna.

Shugaban Ƙungiyar ‘Yan Nijeriya Mazauna Sudan (Ɓangaren Dattawa), Dokta Hashim Na’Allah, ya tabbatar faruwar hakan.

Ya ce, “Tabbas, gwamnatin jihohin Kaduna da Jigawa sun kwashe ‘yan asalin jihohin yau.”

Haka shi ma ɗalibi Abdullah Anyuabuga, ya ce “gwamnatin Kaduna ta kwashe ‘yan asalin jihar a yau ta tafi da su.”

Sauran ɗaliban da suka rage a can Masar da jihohinsu ba su samu damar koyi da waɗanda suka kwashe ‘ya’yansu ba, sun nuna damuwarsu, musamman ganin wannan Lahadin ce karshen kwanakin da aka amince a tsagaita wuta a rikicin na Sudan.

A ranar Juma’a aka jiyo Ofishin Jakadancin Nijeriya da ke Sudan ya ce, ranar Asabar za a fara kwashe kashi na biyu na ‘yan Nijeriya da suka maƙale daga Khartoum zuwa Masar.

Hakan na ƙunshe ne cikin sanarwar da Ofishin ya fitar mai ɗauke da sa hannun H. Y. Garko.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *