Ranar Ma’aikata: Gwamnati ta yi amaye ta lashe kan bai wa NLC izinin amfani da ‘Eagle Square’

Bayan kimanin sa’o’i 48 da janye izinin da ta bai wa Haɗaɗɗiyar Ƙungiyar Ƙwadago ta Ƙasa (NLC) na damar amfani da dandalin ‘Eagle Square’ wajen gudanar da taron Ranar Ma’aikata na bana, Gwamnatin Tarayya ta maida wa NLC izin da ta janye don amfani da dandalin.

Ministan Ƙwadago, Sanata Chris Ngige, shi ne ya sanar da maido da izinin a madadin Gwamnatin Tarayya cikin sanarwar da ya fitar mai ɗauke da sa hannun Daraktan Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a na ma’aikatarsa, Olajide Oshundun.

Ministan ya yi amfani da wannan dama wajen kira ga ɗaukacin waɗanda aka miƙa wa gayyata da su halarci taron, ciki har da Shugaban Ƙasa da mataimakinsa, ministoci da sauransu.

Da fari Gwamnatin Tarayya ta bakin Hukumar Birnin Tarayya (FCDA) ta janye izin da ta bai wa NLC don amfani da dandalin na Eagle Square don gudanar da taron Ranar Ma’aikata kamar yadda ta saba duk shekara.

Gwamnati ta ce ta janye izinin ne saboda dalilai masu nasaba da bikin rantsar da Shugaban Ƙasa mai juran gado, Bola Ahmed Tinubu wanda zai gudana ran 29 ga Mayu.

Da take tsokaci kan janye izinin tun farko, NLC ta bakin Babban Sakatarenta, Comrade Emmanuel Ugboaja, ta bayyana dalilin janye izinin a matsayin rashin jin daɗin taron nasu daga ɓangaren gwamnati da kuma rashin damuwa da makomar rayuwar ma’aikatan Nijeriya.

Ta ƙara da cewa, janye izinin ba zai yi wani tasiri a kan ma’aikata ba, amma gwamnati ta shirya sauraron bayanin ƙungiyar a Ranar Ma’aikata mai zuwa.

A cewar Sakataren, “Sun janye izinin kuma ba su son su yi mana bayani, Ministan FCT ya janye izinin da aka ba mu na yin amfani da Eagle Square don bikin Ranar Ma’aikata.

“Kuma a bayyane yake da yawun gwamnati yake magana, hakan na nufin gwamnati ba ta son yi wa ma’aikata bayani.

“Kenan ba su yaba ƙoƙarin ma’aikatan na shekarun da suka yi wajen yi wa ƙasa hidima, don haka ba za mu ji tsoron yaba wa kanmu,” in ji Ugboaja.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *