Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA
Fiye da harshe da haƙori za su iya samun savani don a waje ɗaya su ke da zama, dangantakar shugabanni da waɗanda su ke jagoranta ba kamar ta waɗannan sassan jiki biyu ba ne. Yayin da shugabanni ke can bayan bangwaye masu tsawo da jami’an tsaro na mazurai sun a kare su, talakawa da a ke mulka na can unguwannin ciki n gari ko ma bayan gari ko ƙauyuka har can cikin dazuka.
Shi ya sa ai sasanta sassan biyu ke da wuya saboda nisan tazarar da ke tsakanin su. Gara ma shugaban dimokraɗiyya da zai buqaci a zave shi ko da ta gidan rediyo ko talabijin ne.
Kazalika zai riƙa bayanan zai cika alqawari da kyautatawa talakawa. A na sa vangaren shugaban mulkin soja kan zo da ƙarfin bindiga ne da za a bi shi ko ba a so, sannan ya tura wakilan sa ko wace jiha a bi su ko a na so ko ba a so. Tsarin ya ma wuce kan madafun ikon jihohi har da wasu ma’aikatu da ma cibiyoyin ilimi tun da an samu soja a Nijeriya da ya tava jan ragamar babbar jami’a. Don haka yayin da soja ke amfani da dokar soja da ya ke tsarawa ba tare da tuntuvar kowa ba, farar hula kan bi tsarin mulki ko da ba 100% sannan ya kan tura wasu buƙatu majalisa don dubawa. Majalisa na da ƙarfin tsige shugaban ƙasa don haka za ka ga aƙalla a zahiri akwai martaba juna ko da a badini daya ɓangaren kan zama dan amshin shata.
Sadarwa tsakanin masu mulkin dimokraɗiyya da talakawa ya fi samuwa lokacin yaƙin neman zave inda a nan ɗin ma sai idan mai takarar na ganin ya na da ƙalubale ko ba zai iya kai labari da qarfin gwamnati ba. Kowa ya zauna ya lissafa alƙawuran da ’yan takarar shugaban ƙasa ko gwamna su ka yi daga 1999 zuwa yanzu, shin an cika dukkan alƙawuran ko kashi 50% a ka samu?
Kai a wani wajen bai fi kashi 30% ko 20% a ka cimma ba. Wasu alƙawuran ma sai an haɗa gwamnati biyu zuwa uku kafin samun cika rabin alqawuran da a ka ɗauka. Akwai ma wanda na ji ya na cewa cikin kwarewar siyasa a Nijeriya akwai koyon yaudarar mutane ga abun da sam ba gaskiya ba ne. Masu ɗan kamanta kwatanta yadda ‘yan siyasar Nijeriya su ke su ne masu cewa ba wai shugabannin kai tasye ne ba su da gaskiya ba, a kan samu mugayen faɗawa ne da ke hana ruwa gudu. Wasu kuma na ɗora alhakin rashin taɓuka abun kirki da nazarin nan da ke cewa na wajen fage gwanin kokawa. Ma’ana mai ganin ba a tavuka abun kirki ba, in an bas hi ragama ba zai iya kataɓus ba, ko kuma a lokacin kamfen ɗan takara kan ɗau alƙawura da furta manyan kalmomi amma in Allah ya sa ya lashe sai ya ga ashe bai fahimci dawar garin ba kamar ya na kallon gazawar daga waje ne alhali matsalar babba ce.
Ba za mu rasa jin ma su zayyana Najeriya da rigar siliki b aka saba ta, ta nan ta goce ta can. Shin in haka ne waye zai iya tavuka abun kirki ya gyara Nijeriya ta dawo da arzikin ta, tsaro da zaman tare? Babbar magana wai ɗan sanda ya ga gawar soja. Ba za a tava taruwa a zama ɗaya ba. Abun takaicin yadda burin ’yan siyasa ya birkita Najeriya ta zama zai yi wuya a iya samun madafun iko ba tare da fakewa da bambancin addini, ƙabilanci ko yanki ba. Hatta shi kan sa Bola Tinubu sai da ya tava kawo batun ƙabilanci ko kuma ya tava cewa wannan lokacin sa ne na hawa karagar mulki. In ya ce loakcin sa ne ka ga kuwa ai zai yi duk abu mai yiwuwa a ƙarfin da ya ke da shi wajen hayewa madafun iko.
Kazalika ya ce lokacinsa ne don marawa shugaba Buhari baya har Allah ya sa ya lashe zave a 2015. Shin ’yan arewa na daukar shugaba Buhari ya yi mulki a madadin ‘yan Arewa ne ko wa’adin ’yan arewa? Kowa ya yi nazari ya samo amsar wannan tambaya. Lokaci ya a ƙasar nan da mutane za su riƙa yi wa kan su tambaya da nemawa kan su amsa mai gamsarwa daga abun da ya ke zahiri a ƙasa.
An samu mabambantan ra’ayoyi kan buƙatar da shugaba Buhari ya yi wa jama’a waɗanda su ke ganin ya yi mu su laifi da su yafe ma sa.
A lokacin gaisuwar idin ƙaramar sallah da al’ummar Abuja da a ka canka ƙarƙashin ministan Abuja Muhammad Musa Bello zuwa fadar Aso Rock, shugaban ya nemi afuwar jama’a a kusan shekaru 8 da ya yi ya na mulkin ƙasar kan abubuwan da su ke ganin ba su ji daɗin gwamnatin ba.
Haƙiƙa tun bayyanar wannan labari na neman ahuwa wasu ke cewa Allah ya yafewa kowa yayin da wasu ke mamakin neman afuwar don su na ɗaukar shugaban a matsayin wanda ba ya nadamar duk matakan da gwamnatinsa ta ɗauka, kazalika ya kan toshe kunne daga duk ƙorafe-ƙorafen da jama’a ke yi.
Ko tambaya a ka yi ma sa kan zargin wasu na taka rawa fiye da kima a gwamnatinsa, ya kan ce a kawo shaida ko kuma lamarin sam ba haka ya ke ba, shi ke aikin sa da kan sa. Maganar wasu masu ƙarfin fada a ji ko wuƙa da nama a gwamnati da a ke kira CABALS bai tava zama wani abun sauraro ko muhimmanci a wajen shugaban ba don ya na ganin ba ma wani abu mai kama da hakan.
Ga irin su dattijo Hussaini Gariko da ya sha fafukar ɗan arewa ya zauna kan mulki, ya ce gaskiya ’yan Arewa in ka ɗebe ’yan jari hujja ba su amfana da mulkin shugaba Buhari ba.
Shi kuma kakakin Sarkin Keffi a jihar Nasarawa Yahaya Shafale ya tuno wahalar da mutane su ka sha ne wajen canjin kuɗin da ba a canja ba inda ƙarshe a ka dawo amfani da tsoffin kuɗi bayan mutane sun galabaita. Shafale ya ce wata mata ta rasa ran ta don an qi amincewa a tura kuɗin yi ma ta aiki ta hanyar banki sai dai kuɗi kai tsaye. Jinkirin da a ka samu na kula da matar a Keffi ya yi sanadin mutuwar ta da ’ya’ya uku da ke cikin ta.
Masu wa’azi irin Sheikh Muhammad Kabir Haruna Gombe sun yi wa shugaban fatan alheri da neman yafewar ubangiji. Sheikh Gombe ya yi addu’ar Allah ya yafewa shugaban ga abubuwan da ya gaza aiwatarwa sannan ya yi wa sabon shugaba Tinubu jagoranci don gyara abun da bai yiwu a baya ba.
Shaharerren malamin Islama a Abuja Sheikh Hussaini Zakariyya ya ja hankalin waɗanda su ka lashe zaɓe su tabbatar da cika alqawarin da su ka ɗauka na kamfen na aiyukan kirki don samun tsira a wajen Allah.
Malamin ya ce ’yan siyasa kan rantse da Allah ko ma da duk abun da su ka yi Imani da shi na aikata abun kirki amma ba lalle ne su kan iya cika alƙawarin ba.
Sheikh Hussaini Zakariyya wanda ke jawabin rufe tafsirin watan ramadan a masallacin Othman bin Affan a Wuse II Abuja, ya kawo mafita ga waɗanda su ka lashe zaven cewa su riƙa fitowa su na fadar gaskiya kan abun da su ka ga zai gagare su.
Malamin ya ce duk wani alƙawari a kamfen tamkar amana ce da ’yan siyasar kan ɗauka kuma ba wata dabarar da za ta kuvutar da su in su ka yi yaudara.
Ga shugaba Buhari da zai sauka daga karaga a watan gobe, Sheikh Zakariya ya ce zai taya shi juyayi ne don ba mamaki bai samu cimma alƙawuran da ya ɗauka ba. Malamin ya ƙara da cewa ya na tausayawa shugaba Buhari don a tarihi shi ne shugaban da ya zo a na murna gas hi zai tafi ma a na murna.
Shugaba Buhari dai wanda bai faye zantawa da manema labaru ba tun hayewar sa karaga a 2015 ya yi alwashin mutane za su gani a ƙasa.
Buhari ya ce lokaci ya yi da zai yi bankwana da mazauna Abuja zuwa mahaifarsa kuma zai yi nesa da su ne ba wai don wata damuwa ba; don ya yabawa ƙauna da su ka nuna masa, amma ya na ganin ya dace ya sulale zuwa ritaya.
kammalawa;
Komai nisan dare gari zai waye in ba dai duniyar ce ta kare ko an samu wani ikon Allah ba. A nan za mu lura komai ya yi farko to zai yi qarshe. Duk wanda Allah ya ba wa damar jagoranci ba ma sai shugaban ƙasa, gwamna ko ma kansila ba, to mutum ya kamanta adalci.
Mulkin gidan mutum ma babban mulki ne da a ke son riƙe amana don samun rabauta gobe kiyama. Alheri gadon barci don haka mu shuka shi iya gwargwadon hali don mu ci moriyarsa a lokacin da za mu fi buƙatar hakan. Ba a fafa gora ranar tafiya don in an yi hakan za a iya shan ruwa da ya gauraya da daci marar daɗi.