Rikicin Sudan da tsaron Nijeriya

Ga waɗanda ke yawan kiran a yi yaƙi a Nijeriya su kalli abinda ke faruwa a Sudan. Tun a ƙarshen makon da ta gabata ne tashe-tashen hankula suka ɓarke a Sudan. Ƙarar harbe-harbe a Khartoum babban birnin Sudan da jirage masu saukar ungulu sun yi ta harba makamai a wuraren zaman jama’a, tsawon ƙarshen mako ana gwabza ƙazamin faɗa tsakanin sojoji da dakarun sa-kai.

Asalin faɗan shi ne rikicin da ya daɗe ana takun-saka tsakanin manyan hukumomin soja biyu na ƙasar. Wato asalin sojin Sudan wadda ita ce rundunar soja ta gwamnatin ƙasa baki ɗaya, sai kuma rundunar sa kai da aka kafa da sunan kai ɗaukin gaggawa, a yanzu waɗannan cangarorin biyu ne ke ƙoƙarin kama mulki. Kuma wannan ya jefa talakawa cikin tsananin buwata da ta shafi rayuwa.

Dalilin tashin hankalin a zahirance shi ne gwagwarmayar samun iko tsakanin mutane biyu. Wato mai riqe da mulkin Sudan kuma babban kwamandan sojojin ƙasar, Janar Burhan, a ɗaya vangaren kuma da mataimakinsa na yanzu, shugaban mayaƙan sa kai, Janar Hamdan Daglo, wanda aka fi sani da Hemeti.

A rikicin Darfur, RSF ta ƙona dubban ƙauyuka, da yi wa mata fyaɗe da kuma tauye haƙƙin bil Adama. Dukkan mutanen biyu ne ke da alhakin wannan. Kuma a juyin juya halin 2019, sun kashe masu zanga-zanga.

A cewar Majalisar Ɗinkin Duniya, kusan mutane miliyan 16 a Sudan sun dogara da taimakon jinqai, kusan kashi uku na al’ummar ƙasar kenan ake magana. A cewar ƙungiyoyin agaji, miliyoyin fararen hula na cikin mummunan haɗarin yunwa. Hukumar samar da abinci ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce dole ne ta dakatar da taimakon da ta ke bayarwa saboda faɗan da ake yi an kashe ma’aikatanta uku a faɗan yayin da suke ƙoƙarin raba kayan agaji.

Abin sha’awa ne, musamman a gare mu a Nijeriya, cewa RSF su ne Janjaweed na Sudan ko Larabawa makiyaya masu ɗauke da makamai da goyon bayan gwamnatin Al Bashir don gudanar da aikin kawar da ƙabilanci a yankin Darfur da sauran al’ummomin noma na Negroid domin su kwace filayensu da kuma kwace musu filayensu.

Lokacin da aka kawo ƙarshen yaƙin Darfur da rikicin bil adama, Al Bashir ya kawo Dagalo da dakarunsa 100,000 kusa da gwamnatinsa, da nufin shigar da su cikin rundunar sojojin Sudan na yau da kullum.

Dagalo ya yi kamar yana goyon bayan jama’a ne ya bi sahun Burhan don tsige Al Bashir a lokacin da masu zanga-zangar neman dimokuraɗiyya suka yi wuya a iya tayar da su.

Darasin da ke gare mu shi ne, a tarihi, munanan abubuwa da yawa da ke faruwa a Sudan a ƙarshe su ma suna faruwa a Nijeriya. Abin da kawai ke taimakawa Nijeriya shi ne, savanin yadda ake yi a Sudan inda aka daɗe ana mulkin kama-karya, duk wani yunƙuri na dagula mulkin kama-karya a Nijeriya ya ci tura ya zuwa yanzu.

Amma ya kamata mu tuna cewa muna da Janjaweed namu na gida Nijeriya, da ’yan bindigar makiyaya da sauran ƙungiyoyin da ba su da tushe balle makama, waɗanda kamar Sudan Janjaweed su ke kai hare-hare a duk faɗin Nijeriya, musamman Kudancin Kaduna, Filato, Taraba, Benuwai, Enugu, Ebonyi, Delta, Ribas, Edo da galibin jihohin Kudu maso Yamma.

Idan ba mu ɗauki matakan da suka dace ba, za mu iya fuskantar wani yanayi da manyan hafsoshin yaƙi za su iya yin gaba ko kuma su yi galaba a kan Sojojin Nijeriya su yi wa Nijeriya zagon ƙasa kamar yadda muka sani.

Abin da kawai ake buƙata shi ne Gwamnatin Tarayya ta ci gaba da ƙoƙarin kawar da ’yan ta’addan maimakon akasin haka.