Mun gyara aikin soja a Nijeriya – Shugaba Buhari

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa, an cimma ƙwararan shirin inganta tsaro a Nijeriya, tare da inganta kayan aiki, horar da jami’ai da tsarin jin daɗin jama’a da ya shafi fiye da yara 50,000 na jaruman sojojin da suka mutu.

Da yake jawabi a Abuja ranar Alhamis, a wani bikin da ya samu halartar tsaffin shugabannin ƙasar biyu, shugaban ƙasa, Janar Yakubu Gowon da shugaban ƙasa, Goodluck Jonathan, shugaban ƙasar ya ce, ya kafa aikin ɗaukar sojoji 60,000 a aikin soja, kuma dubbai aka yaye daga makarantar horar da sojoji ta Nijeriya da sauran cibiyoyin tsaro domin tsaurara matakan tsaro.

Shugaba Buhari ya miƙa sabbin tutoci 81 ga rundunonin sojin Nijeriya daban-daban.

Shugaba Buhari, wanda ya amince da tutoci 81 na runfunan Sojoji daban-daban, ya bayyana cewa, ƙarfin yaƙi da sojojinmu ya yi ƙaranci tun a watan Mayun 2015, inda ya qara da cewa, “Duk da haka, bayan shekaru 7, ƙarfin faɗa ya ƙaru matuƙa inda suka zama na huɗu a matsayi a cikin sojojin Afirka kamar na bakwai a 2015.”

Ya ce, shiga tsakani da kasafin kuɗin shekara ga rundunar, a tsakanin shekarar 2020 zuwa 2022 kazai, an samu damar sayo ɗaruruwan motocin yaƙi, dakarun sojoji, tankunan yaƙi.

Shugaba Buhari ya shaida wa taron manyan hafsoshin tsaro, sarakunan gargajiya, da manyan jami’an gwamnati waɗanda suka halarci bikin cewa, samar da jirgin saman soja na ɗaya daga cikin manyan abubuwan da ake cigaba da faɗaɗa aikin sojojin Nijeriya.

Shugaban ya ce, ƙoƙarin da gwamnatin ta yi ya samu sakamako mai kyau tare da bayanan nasarorin da ba a tava samu ba, wanda hakan ya nuna cewa an samu raguwar masu tada ƙayar baya da kuma ƙaruwar waɗanda suka miƙa wuya tare da iyalansu bisa raɗin kansu domin gyara su ta hanyar ‘Operation Safe Corridor’.

A kan ci gaban ababen more rayuwa, shugaban ya ce, gwamnatin ta yi yunaurin shawo kan giɓin gidaje da sauran abubuwan more rayuwa. Yayin da ƙarfin sojoji ya ƙaru, an kai ɗauki na musamman domin gina sabbin bariki da kuma gyara tsoffin.

Shugaba Buhari ya yabawa babban hafsan tsaron ƙasa Janar Lucky Irabor da dukkan sauran hafsoshin tsaro da shugabannin ƙungiyoyin sa-kai bisa jajircewa da sadaukar da kai ga wannan ƙasa.

Shugaban ya bayyana cewa, an gudanar da faretin sojoji na qarshe a shekarar 2007, kuma tun daga wannan lokacin ne aka kafa sabbin runduna tare da gudanar da ayyukan da suka yi daidai da ƙarin alqawurran da rundunar ta ɗauka.