Na’urar ROV ta ƙasar Sin ta kammala nutson mita 4,308 a ƙarƙashin teku

Daga CMG HAUSA

Cibiyar kula da binciken kimiyyar zurfin teku da ayyukan injiniya ta ƙasar Sin ko IDSSE, wadda ke ƙarƙashin cibiyar nazarin kimiyya ta ƙasar Sin, ta ce na’urar nutso cikin teku mai zurfi ta ƙasar Sin ko ROV, ta kammala nutson mita 4,308 a tekun kudancin Sin.

IDSSE wadda ta bayyana hakan a ranar Alhamis, ta ce an yi dakon na’urar ROV da jirgin ruwan dakon na “Exploration-2”, kuma na’urar ROV ta gudanar da ayyuka yadda ya kamata bisa ingancin ƙirar ta, wanda hakan ya nuna na’urar na da ikon gudanar da binciken kimiyya da injiniyanci a ƙarƙashin teku mai zurfi.

Ana sa ran ROV ƙirar ƙasar Sin, za ta riƙa samar da damammakin mika bayanai ga na’ura mai kwakwalwa a fannin lantarki, da sadarwa, da sarrafawa, ta yadda za a iya ci gaba da amfani da ita wajen gudanar da ayyuka masu yawa, da suka shafi binciken kimiyya.

Mai fassara: Saminu Alhassan