NDLEA ta kama hodar iblis ta biliyan N4 a Legas

Spread the love

Jami’an Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun ƙwayoyi ta Nijeriya, NDLEA sun ce sun kama wani mutum ɗauke da hodar iblis mai nauyin kilogiram 19.4 da kuɗinta ya kai naira biliyan huɗu da miliyan 606.

NDLEA ta ce mutumin ya taho ne daga ƙasar Ethiopia inda kuma ya sauka a filin jirgin sama na Legas, kuma a nan ne jami’an hukumar suka yi ram da mutumin ranar Talata.

Hukumar ta ce mutumin dai mai shekara 48 ɗan Nijeriya ne wanda aka taɓa aikewa da shi kurkuku bisa tuhumar safarar miyagun ƙwaya a bara, amma ya zaɓi ya biya tara domin gujewa zaman gidan kaso.

Shugaban hukumar Mohammed Buba Marwa dai ya sha alwashin sanya ƙafar wando ɗaya da duk masu safarar ƙwayar a Nijeriya.

By ukarofi