Kotu ta ɗaure magidanci kan satar wa matarsa kuɗi

Spread the love

An tsare wani magidanci mai suna Ola Habila ɗan shekaru 46 da ’yar uwarsa Joy mai shekaru 30 a gidan gyaran hali bisa zargin satar Naira 700,000 na matarsa.

Hakan ya biyo bayan hukuncin da wata kotun majistare da ke ƙaramar Hukumar Kafanchan ta jihar Kaduna ta yanke.

Hukumar NSCDC ce ta gurfanar da su bisa zargin satar kuɗin Janet, matar Ola.

Jami’i mai shigar da ƙara na NSCDC, Marcus Audu, ya shaida wa kotun cewa Janet ce ta kai rahoton lamarin a ofishin hukumar.

Audu ya ce, waɗanda ake tuhumar sun je ɗakin mai ƙarar ne, suka hatgitsa kayanta, suka kore ta daga gidan sannan suka sace mata kuɗi kan wata ƙaramar gardama.

Ya ƙara da cewa, waɗanda ake tuhumar an ce sun sace Naira 700,000 na wadda ta shigar da ƙarar a cikin lamarin.

Mai gabatar da ƙara ya ƙara da cewa, wadda ta shigar da ƙarar ya kai rahoton lamarin ga hukumar NSCDC, kuma da aka gayyace shi, wanda ake ƙara na farko ya ƙi cewa komai inda kuma ya yi ƙoƙarin haifar da wani yanayi a ofishin hukumar.

Ya ce, bisa la’akari da haka, ana tuhumar waɗanda ake zaegi da laifin haɗa baki, aikata laifuka, sata, ƙin yin bayani, da kuma hana ma’aikacin gwamnati gudanar da aikinsa.

A cewarsa, laifukan sun saɓawa sashe na 58, 333, 270, 108, da 113 na dokar laifuka ta jihar Kaduna.

Sai dai a lokacin da aka karanta wa waɗanda ake tuhumar dukkansu sun musanta aikata laifin.

By ukarofi