NDLEA ta kama miji da mata kan zargin mallakar buhuna 360 na tabar wiwi

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Rahotanni na cewa an kama wani mutum, Onun Ikoli, tare da matarsa, Itam Onun, bisa zargin mallakar buhuna 360 na tabar wiwi a Jihar Kuros Riba.

Hukumar Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun ƙwayoyi (NDLEA) ce ta cafke ma’auratan a ranar Talata a ƙaramar hukumar Yakurr a jihar ta Kuros Riba.

Kwamandan NDLEA na jihar, John Anteyi, yayin zantawarsa da Manhaja a Kalaba, ya ce ababen zargin sun yi iƙirarin cewa tabar wiwin wadda nauyinta ya kai tan 4.706, ta wani mutum ce da suke zaman haya a ɗaya daga cikin ɗakunan gidansa.

Ma’auratan sun shaida wa ’yan sandan cewa ba su da masaniyar harkar da mutumin yake yi wanda ba a samu nasarar cafke shi ba a gidan.

Itam Onun, mai kimanin shekara 52, ta musanta cewa tabar wiwin ta su ce, inda ta ce: “Ba mu san komai ba. Shi ne mai gidan.

“Mu dai haya muka karɓa a wurinsa kan naira dubu 50, ba mu san irin wannan harkar yake yi ba. Shi ya kawo kayansa ya ajiye amma ga shi an kama mu kan wannan zargin.”

Kwamandan ya ce kawo yanzu dai hukumar tana ci gaba da bincike domin gano ainihin mallakin kayan.

Kazalika, Anteyi ya jaddada cewa wannan samame na cikin yunƙurin da shugaban hukumar NDLEA na ƙasa, Birgediya Janar Buba Marwa (mai ritaya), ke jagoranta na yaƙar miyagun ƙwayoyi da masu safarar su a faɗin ƙasar.

By ukarofi