Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Sanatan Borno ta Kudu, Ali Ndume, ya buƙaci shugaban ƙasa, Bola Tinubu, da ya sanya yankin yankin Arewa maso gabas cikin wuraren da za a kai wa ɗauki a yayin hare-haren haɗin guiwar Nijeriya da Amurka domin fatattakar ‘yan ta’adda.
Ndume, wanda ɗan jam’iyyar APC ne, ya ce, ƙungiyar ISWAP da Boko Haram na cigaba da zaman dirshen a yankin Arewa maso gabas wanda ke nuna buƙatar ɗaukar matakin soji a kansu musamman ta yi masu luguden bamabamai.
A cikin jawabin da ya gabatar a ranar Asabar, sanatan ya yi maraba da ofureshan ɗin yaƙi da ta’addanci na Amurka sai dai ya ce, yakamata a faɗaɗa samamen zuwa yankin Arewa maso yamma.
“Muna maraba da wannan haɗin guiwa tsakanin Nijeriya da Amurka wajen ragargaza maɓoyar ‘yan bindiga.”
“Ina kira kan a faɗaɗa wannan samame da ake kai wa zuwa yankin Area maso gabas inda ISWAP da Boko Haram inda suke da sansanoni uku – Tafkin Chadi da Mandara Mountain da dajin Sambisa – wadanda nan ne inda suka fi ƙarfi,” ya bayyana.
Manhaja ta rawaito muku yadda Nijeriya da Amurka suka kai wani hari ta sama na haɗin guiwa ƙananan hukumomin Tangaza da Tambuwal a jihar Sakkwato.
Samamen dai an kai shi ne a ranar Kirsimeti kan wasu warare da ake kyautata zaton maɓoyar ‘yan ta’adda ne masu biyayya ga ISIS a kan iyakar Nijeriya da Nijar.
Harin dai wanda aka kai ta amfani da sashen ayyukan sojin Amurka a Afirka (AFRICOM), hari ne na hadin guiwa tsakanin sojojin Nijeriya da sojin Amurka bayan Nijeriya ta samar da bayanan sirrin da ake da buƙata.
A shekarun baya ne da ake samu sake ɓullar ‘yan ƙungiyar Lakurawa a Tangaza waɗanda asalinsu sun ɓullo ne daga ƙasashen da ke yankin Sahel. Sun zo ne da farko domin fatattakar ‘yan bindiga da suka addabi al’ummar Sakkwato kafin daga baya su rikiɗe zuwa ƙungiyar ta’addanci ta hanyar ɗora wa al’umma haraji da yin shari’a da samun saɓani da shugabannin garuruwan.
Wani jami’in sojin Amurka, ya shaida wa jaridar The New York Times cewa Amurka ta harba makamai masu linzami kusan 12 samfurin Tomahawk daga jirgin ruwan yaƙin da ke tekun da ake kira da Gulf of Guinea.
Amurka ta ce wannan hari dai ya kashe wasu ‘yan ta’adda da dama.
Ministan harkokin wajen Nijeriya, Yusuf Tuggar, bayan kai harin, ya tabbatar da cewa shugaba Tinubu ne ya ba da izinin kai harin bayan Nijeriya ta ba da bayanan sirri kan inda za a kai harin.
Ndume ya buƙaci gwamnatin tarayya tabbatar da cewa haɗin guiwarta da Amurka bai tsaya kan kai hari ta sama ba kaɗai.
Ya buƙaci a samu horaswa da musayar bayanan sirri da kayayyaki da amfani da jirage masu saukar ungulu domin tallafa wa dakarun Nijeriya wajen yaƙi da ta’addanci.
“Ina so na ba da shawara kan cewa akwai buƙatar samun haɗin guiwa da Amurka wajen faɗaɗa ayyukanta su haɗa da horas da dakarunmu da musayar bayanan sirri da kayayyaki. Sannan a haɗa da tallafa wa dakarunmu da jirage masu saukar ungulu,” ya faɗa.
A yayin da yake magana kan harin bam na masallacin Gamboru, Maiduguri wanda ya yi sanadin mutuwar mutane biyar, sanatan ya ce miƙa ta’azziyyarsa ga iyalan waɗanda suka rasa rayukansu.
“Hairn masallacin Gamboru wata ‘yar manuniya ce kan cewa ‘yan ta’adda ba ruwansu da addini.
“A wannan lokaci na Kirsimeti, Musulmai ma wannan ta’addanci ya shafe su. Don haka, labarin kisan kiyashin kiristoci ba gaskiya ba ne. ‘Yan ta’addan da ke addabar mutane, ba ruwansu da wani addini.”
