Ina kan kujerar gwamna na taɓa wanke bandakin jirgin sama  — Obi

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

Peter Obi, ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Labour a zaɓen 2023, ya ce jagoranci ta hanyar kyakkyawan misali na da matuƙar muhimmanci wajen fuskantar ƙalubalen tsaro da ke addabar Nijeriya.

Obi ya faɗi hakan ne yayin da yake amsa tambayoyi daga ‘yan Nijeriya daban-daban a wani taron tattaunawa na ɗ Space da aka gudanar a ranar Lahadi.

Tsohon gwamnan Jihar Anambra ya ce harkar tsaro ta taɓarɓare matuƙa, kuma tana buƙatar shugabanni masu nuna ɗa’a, nauyi da ɗaukar alhaki.

Da yake amsa tambaya kan yadda zai magance matsalolin tsaro, Obi ya ba da labarin wata ƙwarewa ta kansa domin nuna irin salon jagorancinsa.

Obi ya ce ya taɓa tafiya da jirgin British Airways a lokacin da yake gwamna, inda ya tarar da bayan gidan jirgin sama cikin mummunan yanayi.

A cewarsa, wata mata da ke aiki da gwamnatin Jihar Lagos a zamanin Babatunde Fashola ta buɗe bayan gidan, ta ga yadda yake da datti, sai ta juya ta tafi.

Obi, wanda a wancan lokaci gwamna ne, ya ce ya shiga bayan gidan ya tsaftace shi da kansa ba tare da sanar da kowa ba.

By ukarofi