Neja ta nemi haɗin gwiwar Dangote wajen haƙo mai a tafkin Bida

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Gwamnatin Jihar Neja ta yi kira ga kamfanin Matatar Dangote da sauran masu zuba jari daga ɓangaren kamfanoni masu zaman kansu da su binciki damar da ta ke akwai a wajen haƙo ɗanyen mai a yankin Tafkin Bida da ke jihar.

Kwamishinan Kasuwanci, Zuba Jari, Masana’antu da Bunƙasa Kamfanoni Masu Zaman Kansu na Jihar Neja, Alhaji Aminu Suleiman Takuma, ne ya bayyana hakan yayin wata tattaunawa ta musamman da aka gudanar da kamfanin Dangote a bikin Kasuwanci na ƙasa na Jihar Neja da aka kammala kwanan nan a birnin Minna.

A cewarsa, gwamnatin jihar na haɗa gwiwa da masu ruwa da tsaki daga ɓangaren masu zaman kansu ta hanyar tsarin “One-Stop-Shop” na zuba jari domin bunƙasa damar da jihar ke da ita wajen hako ɗanyen mai.

Takuma ya bayyana cewa gwamnatin jihar na da niyyar riƙe ƙaramin kaso ne kawai a cikin aikin ta hanyar tsarin haɗin gwiwa tsakanin gwamnati da masu zaman kansu wato “Joint Venture-Public Private Partnership (JV-PPP).”

Kwamishinan ya yaba wa Dangote Group bisa ƙoƙarin da take yi wajen bunƙasa masana’antu a Nijeriya, musamman gina matatar mai mafi girma ta nau’in “single-train refinery” a duniya.

Ya ƙara da cewa Jihar Neja a buɗe take ga harkokin kasuwanci, kuma gwamnatin jihar ta ƙuduri aniyar ci gaba da aiwatar da manufofin da za su jawo masu zuba jari a muhimman sassa daban-daban na tattalin arziki.

Daraktar Yanki kuma Babbar Mai Bai Wa Shugaban Kamfanin Dangote Shawara, Hajiya Fatima Wali Abdurrahman, ta bayyana kamfanin Dangote a matsayin abokiyar hulɗa ta halitta ga Jihar Neja, tana mai nuni da gagarumin jarin da kamfanin ya zuba a harkar sarrafa shinkafa a yankin Wushishi.

Ta kuma yaba wa Gwamnan Jihar Neja, Mohammed Umaru Bago, bisa samar da manufofin da suka dace da masu zuba jari domin bunƙasa tattalin arziki da ci gaban masana’antu a jihar.

By ukarofi

Leave a Reply