Neman aure: Kowacce ƙwarya da abokiyar burminta

Spread the love

Tare da AMINA YUSUF ALI

Barkanmu da sake haDuwa a wani makon a shafinku na zamantakewa a jaridarku mai farin jini Blueprint Manhaja.

A wannan maudu’i da za mu tattauna a wannan mako, za mu duba yadda ake yawaitar samun  samari da ‘yammata/zarawa marasa aure a garin nan. Kasashen Hausa cike suke da wadannan matsaloli. Kuma kowa ka tava cikin wadannan matasan sai ya ce ai ya rasa miji ko matar aure ne. Wasu lokutan ma har a kafafen sadarwa ko dandalin sada zumunta na yanar gizo daban-daban za ka ga an ba da cigiyar mutum yana neman matar aure iri kaza, ko mai kama kaza. Haka su ma matan sukan boye sunansu na ainahi su tallata kansu a wadancan kafafen don a samo musu irin mazajen da suke bukata. A yanzu haka zaurukan kulla alakar aure sun yawaita sosai a shafukan yanar gizo. 

Amma daga ina matsalar take? Domin yadda maza suke kokawa da rashin samun mace haka mata ke yi. Amma abin mamakin sai a ga mata/maza birjik a danginsu, ko a wajen aiki/sana’a, ko a unguwarsu da sauransu.

Abu na biyu kuma shi ne, sai ka ga namiji yana da ‘yammata birjik, amma duk da haka kullum fafutukar neman matar da zai aura yake yi. Haka mace ma wata za ka same ta da tarin samari birjik, amma ita ma kana taba ta za ta ce ai ba ta samu mijin aure ba. To wai ina matsalar take ne?

Kada fa mu zama abinda wata karin maganar Hausa take cewa: ‘Da magani a gonar yaro…’  Wato mutum yana tare da maganin matsalarsa amma bai gano ba. A nazarin da na yi, na gano cewa, ba wai abokin rayuwa ake rasawa ba, illa dai kawai rashin samun daidaito.  Ga wasu nazari da na yi a kan haka:

Rashin samun abokin rayuwar da ya dace: Wato za ka ga mace da tarin samari birjik amma kuma ba wanda ya kwanta mata a rai. Wato ba wanda ta ji tana yi masa irin son da za ta iya karshe rayuwarta tare da shi. Haka shi ma namijin. Wasu sun ce ma daga zarar ka hadu da irin wannan matar ko mijin za ka ji a jikinka wannan shi ne wanda kake burin haduwa da shi din.

Shi ya sa sai ka ga saurayi yana tsallakawa daga wannan yarinya zuwa waccan amma bai ji wacce ta kwanta masa a rai har da zai sakankance da ita ta zama abokiyar rayuwarsa ta din-din-din ba.

Rashin dacewa/savawar halayyar juna: Kamar yadda na fada a sama, so yana matukar tasiri wajen kulla alakar da za ta kai ga aure. Amma duk da haka, sai halayya ta daidaita ko ta saba. Wasu masoyan sukan iya fara soyayya kan jiki kan karfi, amma sai rashin fahimtar juna ya sa a yi ta batawa.

Karshe dai a zo a rabu. Idan halayya ta zama daya kamar an samu mara hakuri da takwararsa mara hakuri, sai a yi ta sabawa. Daga karshe a rabu. Yawan faruwar haka zai sa a yi ta canza sheka. Har ma daga karshe mutum ya ba da cigiya don samun matar da yake so.

Kwadayi: Akwai matan da suna aamun manema sosai. Amma masu karamin qarfi ne ko tsaka-tsaki. Wadanda take ganin ba tsararrakinta ba ne a aure. Kuma wadanda take buri su zo su aure ta kuma ba su samu ba.

Wasu ma har da karya sukan zo mata amma daga karshe idan bincike ya zurfafa, sai a ga ashe dai basaja ya yi mata. Irin wannan buri yana zaunar da mata da yawa a gidan iyayensu. Wasu daga karshe burinsu ya cika, wasu kuma burikansu ba sa cika. Daga karshe sai ta hakura ta auri wanda ya samu.

Ko kuma idan aka yi rashin sa’a ta samu maqaryaci wanda ya kware a karyar arziki. Haka za ta dauki kara da kiyashi da hannunta. Kazalika shi ma namiji mai burin auren mace mai maiko yakan dade a kasa bai samu shiga ba. Wani zai ta hankoron ‘yar mai kuxi ko wata attajirar bazawara ko wacce aka mutu aka bar mata Dukiya.

Amma sai ka ga shi a tsarin halitta da halayyarsa kwata-kwata ba ta iya jan ra’ayin wadancan mata da yake ta hankoro. Sai ka ga yana ta lalube don cikar burinsa. Idan bai samu ba sai ka ga ya baza komarsa a wajen masu dalili na zahiri da na zaurukan yanar gizo ko za a dace.

Fasalin mace ko namijin da ake so: kamar yadda Bahaushe yake cewa, wai shan koko daukar rai, ra’ayin mutum yana tasiri matuqa wajen zadar abokin rayuwar aure. Kowanne an’adam, walau mace ko namiji yana da ra’ayinsa game da wanda ko wacce zai aura. Sai qalilan wakanda suke duba halayyar wanda za su aura.

Su  ajiye ra’ayin nasu a gefe. wasu matan sun fi son kyakkyawan namiji ko su ce dogo, wasu su ce sun fi son mai saje, wasu kuma su ce  fari ko baki da sauransu. Hakan su ma mazan sukan ce sun fi son fara, ko baka, ko mai tsawo, ko gajera, ko siririya, ko mai kiba, da sauransu.

Amma inda matar ke ka da mijin shi ne, ita wacce kake son kai ka yi mata? Ko ke wanda kike ra’ayin ina za ki samo shi? Shi ya sa sai a yi ta lalube wani a dace a kusa, wani a samu jinkiri sannan a dace, wani ma kuma sai dai a hakura da abinda ya samu.

Za mu ci gaba a wani makon insha’Allah.

By Editor