An gudanar da taron ƙara wa juna sani don bunƙasa cigaban kiwon kifi a Kano

Spread the love

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano

Ƙungiyar masu noman kifi na Nijeriya reshen jihar Kano “Practicing fish famers association of Nijeriya”ta gudanar da taron wayar da Kan manoman kifi da qaddamar da sabuwar kasuwar kifi a Kano.

Shugaban kungiyar na Kano Alhaji Nura Uba Ramadan ya ce sabuwar Kasuwar ta zo da sabon tsari ba kamar na baya ba. Yanzu an daidaita farashin kifi bai daya da biyan kudi nan take da samar da Manhaja na saye da sayarwar kifi da kaiwa inda ake bukata.

Ya koka da cewa yanzu harkar kiwon kifi ana samun koma baya ne,dan haka suka mai da hankali dan samun mafita, don bayan janye tallafin mai a kasar nan komai ya tashi amma kifi farashin sa bai tashi ba, hakan ya jawo manoma in suka sayar da kifin sai su daina harkar.

Ya ce, wannan dalilin da kalubale ne ya zaburantar da su suke neman hanyar da yakamata manoma su bi domin a samu cin gajiya da zai taimaki cigaban harkar su.

Ya bayyana cewa, an kafa kungiyar ne a 2019 aka yi mata rijista a watan janairu na 2020 yanzu haka suna da mambobi da suka kai 600 a Kano.

Nura Uba Ramadan ya ce abinda suke fata a kungiyar shi ne har kullum harkar kifi ta havaka, domin bukatar da ake na kifi a kasar nan na 4.6mt ne, amma 2.6mt daga waje ake shigo dashi, burinsu idan Allah ya yarda wanda ake shigowa dashi ma daga waje su iya noma shi a gida.

Ya ce, a bara sunada tsari da suka fito da shi yadda za a yi amfani da dama-damai da suke Kano da suke so ayi wani aiki tsakanin su Gwamnatin Tarayya da ta jiha, amma ba’a zo gava ta aiwatarwa ba Gwamnatin baya ta tafi,amma yanzu tunda komai ya kankama, anyi sabuwar Gwamnatin Tarayya an yi minista an sami sabuwar Gwamnati a Matakin Jihar Kano an yi sabon kwamishina dan haka zasu sake karkade takardun su sake bibiya.

Alhaji Nura Uba Ramadan ya ce harkar noman kifi na bada gudummuwa sosai wajen samarda aiki ba kawai ga maza ba, mata a cikin gidaje suna kiwon kifi sosai hakan na mutuqar rage zaman rashin aikin yi a tsakanin al’umma.

A yayin taron da aka gabatar karkashin jagorancin Uban taron Alhaji Ado Muhammad shugaban rukunin gidajen Radiyon Freedom an gabatar da kasidu daga masana daban-daban akan matakai da masu noman kifi za su dauka domin bunkasa cigaban nomansu na kifi.

By Editor