Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano
A ranar Talatar da ta gabata ne kungiyar Lore na masu sayar da babura da ke kasuwar ’yan babura a kan titin Murtala Muhammad ta gudanar da zaben sabbin shugabaninta.
Zaben da Alhaji Bilya Ubale Muktar ne ya yi nasarar zama sabon shugaban kungiyar ta Lore da yawan quri’u 380 da aka kada hakan tasa ya sami nasara akan abokin takarar sa Alhaji Husaini M.Y.Abdullahi Fagge da ya sami kuri’u 128.
A mukamin mataimakin shugaban kungiyar Ashiru Abubakar shine ya sami nasara ba tare da hamayya ba, haka ma sauran matakai na zaben na muqamai daban-daban duk yan takararsu sun yi nasara ba tareda hamayya ba.
Wakilin ma’aikatar ciniki, masana’antu da kungiyoyin gama kai na jihar Kano da ya jagoranci gudanar da zaben. Daraktan Mulki da sauran ayyuka na ma’aikatar Alhaji Bello Abdullahi ya ja hankalin yan kungiyar da cewa su zauna lafiya su bada goyon baya ga wadanda sukayi nasara, su kuma su sabbin shugabanni da aka zaba su riqe qungiyar bisa adalci da kula da al’umma kowa ya zama nasu ba tare da nuna bambamci ba.
Sabon zababben shugaban na kungiyar ta Lore na Kasuwa yan Babura na Fagge. Alhaji Bilya Ubale Fagge ya yi godiya ga Allah bisa nasara da ya samu da yabawa da irin goyon baya da yan kasuwar suka bashi.
Ya ce, dama su ’yan kasuwar ne Kuma suna tare da kungiyar da ba ta gudunmuwa tsawon shekaru suna kuma lura da matsaloli da ke addabar ta da suke so su sami dama da za su taimaka don ganin ta tsaya da kafafunta, wannan na daga dalilin fitowar sa yin takarar.
Ya yi nuni da cewa duk harkar shugabanci yana tare da kalubale, wadanda suka jagoranci kungiyar a baya kowa da irin yanda ya tafiyar da nasa, yanzu da aka zabe su suke so suma su dora akan irin kokarin da na baya suka yi domin su kawo sauyi na dora kungiyar ta sami cigaba da ba ta tava samu ba.
Alhaji Bilya ya ce za su tabbatar da da’a da bin doka da oda a harkokin kasuwar da kuma tabbatar da kungiyar ta tsaya da kafarta, sannan ya yi kira ga wadanda suka yi takara ba su yi nasara ba, su zo a hadu domin bunqasa cigaban kungiyar.
Ya ce, za su nemi hadin-kan Gwamnatin Kano ta bijiro da abubuwa da za su ragewa ita kanta hukuma nauyi na aikin da take a karkashin kungiyar da za ta yi farin ciki da hakan.
Alhaji Bilya Ubale ya jaddada cewa a wannan lokaci da za su jagoranci kungiyar ta Lore za su tabbatar da da’a da bin doka da oda kuma suna fata ’yan kungiyar da suka zabe su a matakai daban-daban su basu cikakken hadin-kai da goyon baya don bunkasa cigaban Kasuwar na yan babura
