NGE ta shirya gudanar da babban taronta a Kano

Daga FATUHU MUSTAPHA

Kungiyar Editoci ta Nijeriya (NGE) ƙarƙashin jagorancin Comrade Mustapha Isah, ta sanar da cewa ta yanke shawarar gudanar da babban taronta na ƙasa a birnin Kanon Dabo.

Comrade Mustapha Isah, ya ce ra’ayin gudanar da babban taron ƙungiyar a Kano ya zo a daidai lokacin da ya fi dacewa.

Da yake zantawa da manema labarai jim kaɗan bayan kammala naɗa kwamitin tsare-tsare, shugaban ƙungiyar ya ce Kano wuri ne mai zaman lafiya wanda mambobin ƙungiyar ba za su samu wata fargaba ko tsoron zuwa ba daga ko’ina don halartar taron.

Ya ce kwamitin da aka kafa mai mambobi 7 ƙarƙashin jagorancin Dr. Sule Yau Sule, an ɗora masa alhakin nema wa baƙi masauki da abincin da za a ci yayin taron, tare da samar da wurin da taron zai gudana da dai sauran tsare-tsaren da su taimaka wajen cim ma nasarar gudanar da taron.

Da yake tofa albarkacin bakinsa a madadin mambobinsa, shugaban kwamitin Dr. Sule Yau Sule ya ce Gwamnatin Jihar Kano za ta sa wa ƙungiyar hannu don tabbatar da cewa komai ya tafi daidai kamar yadda aka shirya.

Dr Sule ya bayyana cewa kwamitin na sa ran soma karɓar mambobin ƙungiyar ya zuwa 26 ga Afrilu, 2021.

Yana mai cwa, “Taron zai gudana ne a ranar 27 ga Mayu, yayin da rangadin duba ayyukan Gwamnatin Kano zai gudana a ranakun 28 da 29 ga Mayu, 2021.

Kwamitin ya ce zai gana da Mataimakin Gwamnan Jihar domin tsara yadda rangadin zai gudana.

A ƙarshe, Dr. Yau ya yi kira ga ‘yan jarida da su bada himma wajen wayar da kan al’umma game da ayyukan NGE.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *