An kama hanyar bai wa wasu marayu ilimi mai nagarta a Gombe

Daga ABUBAKAR A. BOLARI, Gombe

Shugaban gidauniyar zaka da waƙafi na jihar Gombe, Abdullahi Abubakar Lamiɗo, ya yi alƙawarin cewa gidauniyarsu da gidan Marayu na AL-GUH (Al- gidan Umma Hajara) za su haɗa kai dan ganin an bai wa marayu ilimi mai inganci dan su samu abun dogaro a rayuwa.

Abudullahi Lamiɗo, ya bayyana hakan ne a lokacin da tawagar gidauniyar suka ziyarci gidan marayun a ranar Lahadi dan ba su tallafin kayan abinci cikin irin tsarin su na tallafa wa gajiyayyu da marayu a watan Ramadan.

Ya koka kan irin yadda Musulunci yake da tsari ya kuma bayyana falalar taimaka wa maraya amma wasu ba sa iya kula da maraya balle su ɗauki nauyin sa.

Shugaban gidauniyar ya bada shawarin cewa a samu wani tsari da za a samar wa marayun ilimi mai inganci na addini da na boko saboda shi ne abun da za a yi musu su samu madafa a lokacin da suka girma, yana mai cewa idan ba a ba su ilimi mai nagarta ba, ba a taimaki rayuwarsu ba.

Da take mayar da jawabi jigo daga cikin masu kula da gidan marayun, Hajiya Aisha Yahaya Muhammad, cewa ta yi da a gidan na AL-GUH suna da marayu guda 15 da suka kwaso daga wajen ‘yan gudun hijira da suka fara girma sai mazan suke ba su ciwon kai wajen kulawa da tarbiyar su, ganin kar su lalace a wajen su ya sa suka nemi ‘yan’uwan su suka mayar da su amma yanzu matan da suke da su ba su fuskantar wata matsala da su.

Hajiya Aisha Muhammad, ta ce gidan bai samun kulawa daga masu hannu da shuni sai ɗaiɗaikun mata suke yawan ziyartar gidan galibi sai cikin azumi kamar yanzu, kuma idan azumi ya wuce ba su samun tallafi sosai.

Tawagar gidauniyar sun je gidan ne a zagayen da suke yi wajen raba kayayyakin masarufi na tallafi da suka saba bayarwa, a nan ne suka yi alƙawarin haɗa kai don kulawa da ilimin marayun.

Gidauniyar ta raba kayayyakin masarufi wa mutane fiye da 700 amma burinsu shi ne su tallafa wa magidanta dubu biyar da abin da za su ci a wannan wata na azumi.

Daga nan Abdullahi Lamiɗo, ya ce da sun gama raba kayan azumin za su fara shirin raba wa marayun kayan sallah domin aikin kenan kullum, bayan kuma ita wannan gidauniyar tana zaɓo mata marasa galihu da waɗanda suke da nauyi na marayu a kansu suna koya musu sana’o’in hannu daban-daban suna kuma tallafa musu da jari.