Za a yi jana’izar mahaifiyar Sarkin Kano yau

Daga BASHIR ISAH

Masarautar Kano ta bada sanarwar za a yi jana’izar mahaifiyar Sarkin Kano, marigayiya Hajiya Maryam (Mai Babban Ɗakin Kano), a yau Litinin.

Masarautar ta bayyana haka ne cikin wata sanarwa da ta sami sa hannun Madakin Kano, Yusuf N. Ibrahim Chigari da aka fitar a jiya Lahadi.

Sanarwar ta ce, “A bisa babban rashi da muka yi na rasuwar Mai Babban Ɗakin Kano, wanda ya faru Asabar 12 ga Ramadan 1442 (24 ga Afrilu, 2021)
a ƙasar Masar, Masarautar Kano da Masarautar Bichi, na sanar da shirin
jana’iza kamar haka: Ana tsammanin isowar mamaciya filin jirgin saman Malam Aminu Kano a yau (jiya Lahadi) 13 Ramadan, 1442 (25 Afrilu, 2021) bayan Magriba.

“Za a yi sallar jana’iza a gobe (yau Litinin)14 Ramadan, 1442 (26
Afrilu, 2021) da misalin ƙarfe 11 na safe, a Ƙofar Kudu, Fadar Mai Martaba, Sarkin Kano.

“Za a kai mamaciya hubbaren Gidan Sarkin Kano. Muna addu’a Allah Ya gafarta mata, Ya yi mata Rahama tare da magabatanmu, da dukkan Musulmi.”

Hajiya Maryam ta rasu tana da shekara 86 a duniya. Kuma ita ce mahaifiyar Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero da Sarkin Bichi, Alhaji Nasiru Ado Bayero.

Manhaja ta kalato cewa marigayiyar tsohuwar matar marigayi Sarkin Kano ce kuma gimbiya a masarautar Ilorin a jihar Kwara.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *