Nijeriya a hannun ’yan jari hujja (2)

Abinda nake so jagororin al’umma su sani shi ne, tsanani ba ya sa al’umma ta gyaru, haka nan duk lokacin da na sama ya danne na ƙasa, to zai yi ƙoƙarin ƙwatar kansa ne, dazarar kuma ya samu kansa, to ba zai yarda a ci gaba da danne shi a ƙasa ba. Har yanzu lokaci bai ƙure muku ba, ku jagororin al’umma. Kuna da lokacin da za ku gyara, ku tsaya ku yi nazari da duban halin da al’ummar ƙasa suke ciki sannan ku yi abinda ya dace, ku yi abinda shi ne daidai. Amma a yanayin da ƙasar nan take tafiya da sunan ana mulkin ‘yanci, mulkin siyasa da sunan Dimokuraɗiyya, ko shakka babu hakan ba zai haifar da ɗa mai ido ba.

Abin kunya da takaici ne a ce, kowanne ɗan majalisa da Sanata, Ministoci da sauran jagororin al’umma su ƙauracewa yankunansu da jihohinsu, suje su tare a Abuja da sunan suna wakiltar al’umma, amma ba su damu da su san halin da al’ummar da suke wa wakilci halin da suke ciki ba, sai lokacin siyasa ya juyo su dawo gare su babu kunya babu tsoron Allah, su kuma nuna cewa suna son su sake zaɓarsu su koma kan muƙamansu. Ko kaɗan wannan bai zamo adalci ba, bai zamo sauke nauyi ba, haka nan bai zamo abin alfaharin da wakilai za su bugi ƙirji su kiran kansu wakilan al’umma ba.

A halin da muke ciki a yau a ƙasar nan, an ga yadda ’yan ƙasa suka riƙa fitowa fili suna nuna buƙatarsu ga sojoji a kan su karɓi ƙasar nan.

Wannan yana nuna akwai rashin buƙatar mulkin dimokuraɗiyyar ga su ‘yan ƙasa, tunda gashi suna neman sojoji su karɓe mulkin daga hannun farar hula. A tafiyar da ake yi a halin yanzu, babu tabbacin cewa ‘yan ƙasa za su sami sa’ida, domin babu wanda yake jin kokensu, waɗanda suke amsa sunan manya kuma dattawan ƙasa, tare da wakilan al’umma, kowa ya kauda kansa daga kan talakawa. Idan talaka yayi ku ka babu wanda zai saurare shi, amma idan yayi bore sai a kama shi, ko a harbe shi, ko a kira shi da ɗan ta’adda ko tawaye ga gwamnati.

An lalata yankin Arewa, an kassara ci gabanmu, amma duk manyan Arewan sun yi gum da bakunansu. Ana shaƙa musu kuɗi da daɗɗaɗan abinci ta sama, yayin da su kuma suke shaƙa wa talakawa guba ta ƙasa suna faɗuwa suna mutuwa. Doka bata aiki ga kowa sai talaka, jami’an tsaro basa nuna ƙwanjinsu ga kowa sai talaka. ‘Yan siyasa suna amfani da raunin talakawa suna saye ƙuri’unsu, suna buga kansu tare da saka musu gaba da ƙyamar juna. Suna amfani da matasa wajen bangar siyasa da tada-zaune-tsaye.

ɓarayin gwamnati masu manyan riguna da manyan aljihu, suna ɗibar kuɗin al’umma sun bushasharsu yadda suke so, suna gina rayuwar ‘ya’yansu da matayensu haɗi da ‘yan uwa, amma su talakawa da ‘ya’yansu an maida su ‘yan baranda da bangar siyasa, an maida su sojojin baka a kafafen watsa labarai, an maida su ‘yan ta’addar siyasa, ana basu kuɗin da bai taka-kara-ya-karya ba, su sha miyagun ƙwayoyi, a basu makamai su fito kan titi suna ihu da layi tare da muzurai suna zare idon sai wane. A daidai lokacin babu ɗansa ko wani nasa a cikinsu, iyalansa suna can a killace, wataƙil ma abinci mai rai da lafiya haɗi da nama suke ci, ga ruwan roba da lemuka a gefensu, sun kunna talabijin ma suna kallo, ga sanyin AC na ratsa su, ga kuɗaɗe a cikin aljihu da asusun banki, ga ƙaton gida da motoci masu tsada, duk abinda suke so kiran waya ɗaya ya wadatar a azo ayi musu ko a kawo musu. Amma kai talakan Nijeriya kana can cikin rana, ga yunwa, ƙishin ruwa, kana kware baki kana sai wane ko a mutu duka.

Lokaci yayi da matasanmu ya kamata su dawo daga rakiyar duk wani ɗan siyasa wanda ba shi da fatan alkhairi a gare su, kowa yasan ciwon kansa. Sannan ya kamata matasan Nijeriya su ɗauki izina ga zaɓen ƙananan hukumomin da aka yi a jihar Kano na ranar 26 ga watan Oktoba, 2024. Zaɓen da ba ayi tsammanin za a yi shi ƙalau ba, amma saboda kiraye-kirayen da aka yi wa al’umma, tare da ƙara wayar musu da kai, hakan tasa aka yi zaɓen ba tare da wata fitina ba. Kowa yaga ni, babu jami’an tsaron ‘yan sanda balle sojoji, daga ‘Yan Hisba, Karota sai ‘Yan ɓiggilant Group, amma ko Kaza ba a cutar ba.

Wannan ya nuna mana ashe za a iya yin zaɓe ba tare da an yi tashin hankali ba koda babu jami’an tsaro a wajen. To haka ya kamata mu zama, mu san ciwon kanmu, mu daina bari ‘yan siyasa na amfani damu wajen cimma buƙatunsu, a ƙarshe mu kuma su watsar damu.

Batu na gaskiya shi ne, da ‘yan majalisu da sanatoci da dukkan hukumomin gwamnati suna da kishin ƙasa da al’ummar ƙasa a cikin zukatansu, to da abubuwan da suke faruwa a yanzu a ƙasar nan ba za su faru ba, idan ma sun farun to sai dai ya zama na ɗan lokaci amma ba wanzu har kawo yanzu ba. Don haka, tilas ne mu ‘yan ƙasa mu nema wa kanmu mafita ta dukkan hanyoyin da suka dace. Wajibi ne muyi kishin kanmu da ƙasarmu, muyi kishin jahohinmu, muyi kishin garuruwanmu, mu tashi tsaye mu nemi ‘yancinmu don dawo da martabar ƙasar nan. Yin zanga-zanga ba mafita ba ce, yin faɗa da gaba duk ba su ne za su kai mu gaci ba. Mu haɗe kanmu, mu nuna kishin junanmu, mu watsar da duk wata barazana ko saka mana fargaba da tsoro da ake yi. Mu ‘yan ƙasa ne, muna da haƙƙi a cikinta, sannan dole mu tuna goben ‘ya’yanmu da za su taso a bayanmu.

Ko kusa ko alama, ni banga wata hanyar samun sauƙi a irin wannan salon mulkin da ake yi a Nijeriya na yanzu ba, domin kullum al’amurra ƙara ta’azzara suke yi. ‘Yan ƙasa sun shiga mawuyacin halin da, ba kowa ne yake iya jurewa ba. Kuma babbar illar hakan ita ce, duk wanda ya ji matsi yayi yawa, to ba ya buƙatar a ce masa ga yadda zai yi ya samu mafita, in ma dai ya zamo ɗan ta’adda ƙasa ta ƙara lalacewa, ko kuma ya zamo na kirki wanda hakan zai yi wuya, ko kuma zuciyarsa ta buga ya mutu saboda takaici da baƙin cikin halin da shugabannin ƙasarsa suka jefa su.

Da wannan nake ƙara yin kira ga mahukunta a ƙasar nan, jagororin al’umma daga ƙasa zuwa sama, attajirai da duk wani mai faɗa aji, lallai ya kamata a tashi tsaye ayi abinda ya dace don raba ‘yan ƙasa da uƙubar da suke ciki. Wannan ita ce kaɗai hanyar da ta rage wajen dawo da martabar ƙasar nan, amma wallahi idan har aka yi sake al’umma suka kai ƙarshe, tura ta kai bangon ƙarshe, to hakan ba zai haifar muku (ku shugabanni) da ɗa mai ido ba. Don haka kuji tsoron Allah, ku tuna cewa ƙasar nan ba taku ba ce ku kaɗai, arzikin da yake cikinta ba gado ku ka yi ba, arzikin ƙasa na al’ummar ƙasa, Musulmi da Kirista kowa yana da haƙƙi. Saboda haka ku yi abinda ya dace.

Ba mu da ƙasar da ta wuce Nijeriya, kishin ƙasa wajibi ne, sauƙaƙa al’amurra don ‘yan ƙasa suyi rayuwa cikin aminci kuwa, idan shugabanni sun yi wannan sauke nauyi ne. Idan kuma ba su yi ba, to Allah zai tara kowa a gabanSa ranar sakamako. Hatta da Akuyar da take da ƙaho ta soki ‘yar’uwarta sai Allah Yayi hisabi a tsakaninsu. Kuma duk kuɗinka, mulki da sarautarka, taƙama da isa gami da tunƙahonka, za ka mutu, za a binne ka kai kaɗai ba tare da kowa da komai ba, sannan ranar Alƙiyama za a haɗu gaban Allah, kuma wannan tabbas! Dahir! Sai ta faru, babu kokwanto a ciki.

Daga NAFI’U SALISU.


Marubuci/Manazarci, daga Kano Nijeriya. [email protected]
[email protected]. 08038981211-09056507471.