Nijeriya ce ta biyu a yawan mace-macen mata masu ciki

Rahoton Hukumar Kiwon Lafiya ta Duniya (WHO) ya ce, yanzu Nijeriya ita ce ƙasa ta biyu a jerin ƙasashen da ke da yawan mace-macen mata masu juna-biyu a duniya.

A cewar rahoton, Nijeriya ke da kashi 29 daga cikin adadin 290,000 na mace-macen mata masu jina-biyu da ake samu duk shekara.

Kazalika, Nijeriya ce kan gaba a faɗin duniya wajen aukuwar mutuwar jarirai da ƙananan yara in ji rahoton.

WHO ta lissafo wasu ƙasashen da ke fuskantar yawan mace-macen mata masu ciki, jarirai da kuma ƙananan yara da suka haɗa da Pakistan, Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo, Habasha, Bangladesh, China, Indonesia, Afghanistan da kuma Tanzania.

Hukumar ta yi gargaɗin duba da yadda al’amarin yake a halin yanzu, sama da ƙasashe 60, ciki har da Nijeriya, ka iya rasa cimma ƙudirin rage mace-macen mata masu juna-biyu, jarirai da ƙananan yara kamar yadda yake ƙunshe cikin manufar shirin ‘Sustainable Development Goals’ ya zuwa 2030.

Sauran ɓangarorin da WHO ta nuna damuwarta a kai sun haɗa da ƙaruwar talauci, taɓarɓarewar jinƙai da kuma ƙarancin kuɗi da ke ci gaba da addabar ƙasashe a faɗin duniya.