Gwamnatin Nijeriya da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa (UAE) sun shirya tattaunawa domin magance matsalolin da ke tattare da samun bizar tafiya zuwa UAE. Wannan shawara ta samo asali ne bayan da jakadan UAE a Najeriya, Salem Saeed Alshamsi, ya kai ziyarar ban girma ga Ministar harkokin waje, Ambasada Bianca Odumegwu-Ojukwu, a ofishinta da ke Abuja.
Ambasadar ta bayyana cewa akwai kyakkyawar alaƙa tsakanin ƙasashen biyu, inda Najeriya ta kasance amintacciya wajen kula da dangantakar diplomasiyya da UAE. Ta kuma ƙara da cewa birnin Dubai ya kasance wurin da ‘yan Najeriya ke sha’awar ziyarta, inda a shekarar 2015 kadai, ‘yan Najeriya kusan miliyan guda suka ziyarci UAE, suna kashe sama da dala biliyan ɗaya wajen cinikayya da sauran buƙatu.
Jakadan UAE, Alshamsi, ya tabbatar da cewa tun bayan zuwansa Najeriya shekara ɗaya da rabi da suka gabata, ya tabbatar da ƙaruwar bayar da bizar yawon buɗe ido, inda aka raba fiye da biza 700 daga watan Yulin 2024 zuwa yanzu. Ya kuma jaddada cewa akwai yarjejeniyoyi da dama da aka ƙulla tsakanin kasashen biyu da ake ƙoƙarin ingantawa domin bunƙasa haɗin kai da kuma zuba jari.
Ministar ta gode wa gwamnatin UAE kan taimakon kayan agaji da suka kawo domin tallafa wa waɗanda ambaliya ta shafa da kuma alluran rigakafin cutar kyanda. Ta bayyana cewa Najeriya za ta karɓi baƙuncin taron kwamitin haɗin gwiwa na gaba domin tabbatar da cika alƙawura da yarjejeniyoyi da aka amince da su.