
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
A wani yunƙuri na ƙarfafa alaƙar kasuwancin da ke tsakaninsu, Nijeriya da ƙasar Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa (UAE), sun soke harajin kayayyaki na sama da guda 13,000 don faɗaɗa damarmakin hada-hadar kayan Nijeriya.
Gwamnatin Tarayya ta sanar da haka a ranar Talata inda ta ce ta soke dukkan harajin kayayyaki 6,243 da ake shigowa da su Nijeriya daga UAE, yayin da ita ma ƙasar ta cire harajin na guda 7,315 na waɗanda shiga su daga Nijeriya a ƙarƙashin yarjejeniyar Nigeria-UAE Comprehensive Economic Partnership Agreement (CEPA).
Ma’aikatar Masana’antu, Kasuwanci da Zuba jari ta bayyana haka dalla-dalla acikin wata takarda da aka sanya wa hannu a Junairun 2026.
A cewar ma’aikatar, yarjejeniyar CEPA za ta faɗaɗa damarmakin damar samun kayayyakin Nijeriya cikin, fagagen kasuwanci da ƙwararru da za su taimaka wajen bunƙasa harkokin zuba jari, lamarin da zai ƙarfafa alaƙar tattali tsakanin ƙasashen biyu.
Ta ƙara da cewa, za a soke harajin kayayyaki 2,294 na tsaron shekaru biyar yayin da za a ware wasu 123 daga sanya musu takunkumin haraji.
A nata ɓangaren, UAE ta yi alƙawarin cire haraji a kayayyakin Nijeriya guda 7,315, waɗanda dafa ciki za a cire wa guda 2,805 a nan take wato kaso 38.3. Ta ce, za a yi hakan ne na tsawon shekaru uku ga 1,468 da cire takunkumin haraji na tsawon shekaru biyar ga wasu guda 3,042.
A ranar 13 ga watan Junairu, 2026 aka ƙulla yarjejeniyar bayan tattaunawa da Ministar Masana’antu, Kasuwanci da Zuba jari, Dakta Jumoke Oduwole da agajin Ma’aikatar Shari’a da Hukumar Kwastom.
Haka kuma, an sanya hannun ne tsakanin Dakta Oduwole da Dakta Thani bin Ahmad Al Zeyoudi akan idon Shugaba Bola Tinubu da Shugaban UAE Sheikh Mohamed bin Zayed Al Nahyan.
