Kawo yanzu an samu tawagar 19 da ta samu gurbin shiga gasar kofin Afirka da za a buga a 2025, saura biyar ake jira su zama 24.
Daga Litinin da Talata za a ƙarƙare sauran wasannin cikin rukuni, inda ake sa ran samun sauran tawagar da za ta je babbar gasar ƙwallon ƙafa ta Afirka ta baɗi.
Za a fara wasannin a Morocco daga 21 ga watan Disambar 2025 zuwa 18 ga watan Janairun 2026.
Tawagar Super Eagles ta Nijeriya wadda ta taɓa lashe kofin nahiyar Afirka har sau uku tana cikin ƙasashe biyar da suka samu tikitin shiga gasar kofin nahiyar Afirka ta 2025 a zagayen kusa da na ƙarshe da aka doka a makon da ya gabata.
‘Yan wasa 10 na Tunisia sun zura ƙwallo a minti na 93 a wasan da suka yi nasara kan Madagascar da ci 3-2 sannan kuma suka kafa tarihi a gasar inda za su buga gasar a karo na 17 a jere.
Gabon da Afirka ta Kudu da Uganda duk sun samu nasu tikitin ba tare sun take wasa ba bayan da sauran sakamakon wasannin rukunan suka dace da abin da suke buƙata.
Nasarar da Libya ta samu akan Rwanda da ci 1-0, ya sa Nijeriya ta samu tabbacin ta zama ta ɗaya a rukunin D tun ma kafin a fara wasansu da Benin.
ɓictor Osimhen ya zura ƙwallo a raga yayin da Super Eagles ta yi kunnen doki da ci 1-1 – sakamakon da ke nufin Benin da Rwanda da Libya duk za su buga wasannin ƙarshe na rukuni da damar zuwa gasar a Morocco.
A halin da ake ciki dai fatan Ghana na neman shiga gasar na nan daram bayan da Sudan ta sha kashi a gidan Nijar da ci 4-0, waɗanda suka farfaɗo da nasu yaƙin neman tikitin.
Ghana wadda ta lashe gasar ta afcon har sau huɗu yanzu ya zame mata dole ta doke Angola wadda ta riga ta samu nata gurbin a Luanda ranar Juma’a domin ci gaba da farautar tikitin zuwa gasar ta 2025.