ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Roma, ta naɗa Claudio Ranieri a matsayin sabon kocinta har zuwa ƙarshen kakar wasa ta bana – watanni shida bayan ya sanar da yin ritaya.
Ranieri ya kuma karɓi muƙamin mai bai wa mahuntan ƙungiyar shawara kuma zai taimaka wajen neman koci na dindindin.
Ranieri, wanda ya jagoranci kulob ɗin sau biyu a baya ciki har da na wa’adin wucin gadi a shekarar 2019, ya yi ritaya ne a watan Mayu bayan ya jagoranci Cagliari a Serie A.
Naɗin nasa ya zo ne bayan korar Iɓan Juric a ranar Lahadi.
Juric ɗan ƙasar Croatia ya buga wasanni 12 kacal bayan ya maye gurbin Daniele de Rossi bayan wasanni huɗun farko na kakar wasan bana. Tsohon ɗan wasan tsakiya na Italiya De Rossi ya riƙe matsayin kocin ne na watanni takwas bayan tafiyar Jose Mourinho a watan Janairu.
Ranieri ya horar da ƙungiyoyi 18 da kuma tawagar ƙwallon ƙafa ta ƙasar Girka a tsawon shekaru 37 da ya yi yana horar da ’yan wasa.
Babbar nasarar da ya samu ita ce kofin Premier da ya ci tare da Leicester City a kakar wasan 2015-16.
Bayan kashe sama da fam miliyan 80 a kasuwar musayar ‘yan wasa ta bazara, Roma tana matsayi na 12 a teburin Seria A da maki 13 bayan wasanni 12, kuma tana mataki na 20 a teburin gasar Europa Leƙague da maki biyar bayan wasanni huɗu.
Wasanta na gaba a gasar Serie A shi ne ziyarar da za ta kai Napoli ranar 24 ga Nuwamba.
