Fitaccen ɗan damben boɗing na duniya da yayi fice a shekarun da suka gabata, Mike Tyson, ya ce ko kaɗan baya nadama akan komawa filin da yayi duk da cewar ya sha kaye a hannun abokin karawarsa Jake Paul mai shekaru 27.
Tyson mai shekaru 58 ya sake gwada ƙarfin da ya rage masa ne yayin karawarsa da Paul ranar Juma’ar da ta gabata a birnin Teɗas dake Amurka.
Bayan shafe tsawon lokaci suna fafatawa, alƙalai sun raba damben na boɗing tare da bayyana Jake Paul a matsayin wanda yayi nasara bayan samun maki mafi rinjaye a turamen faɗan da suka gudana.
Alamu dai sun tabbatar da cewar shekaru sun cimma Mike Tyson, wanda a zamanin da yake matashi ake yi wa laƙabi da Iron Mike, domin kuwa a wannan karon tsohon zakaran damben ya gaza nuna kuzarin da yayi fice da shi a baya, lamarin da bai yi wa dubban masu kallon da suka kwarara garin na Teɗas domin bai wa idanunsu abinci daɗi ba.
Alƙaluman alƙalan wasa sun nuna cewar sau 78 Jake Paul ya samu nasarar naushin Mike Tyson, yayin da shi kume Iron Mike ɗin ya naushi Paul sau 18.
Bayan sa’o’i da kammala wasan ne Mike Tyson ya wallafa sako a shafinsa na ɗ, inda ya ce ba ya nadamar sake komawa filin dambe a karon ƙarshe da yayi, domin a ganinsa shi ke da nasara ko da kuwa alƙaluma sun nuna akasin hakan, domin kaɗan ya rage ya baƙunci lahira a watan Yuni saboda rashin lafiya, to amma sai gashi ya murmure har ma da fafata dambe duk da turawar shekarunsa.