NLC za ta yi zanga-zanga don adawa da ƙarin kuɗin kiran waya

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

Kungiyar ƙwadago ta NLC a Nijeriya ta ce za ta gudanar da gagarumar zanga-zanga ranar Talata 4 ga watan Fabrairun 2025, domin adawa da ƙarin kuɗin kiran waya da kashi 50 wanda Hukumar Sadarwa ta Nijeriya NCC ta amince da shi.

Wata sanarwa da ƙungiyar ta hannun shugabanta Joe Ajaero, ya ce sun ɗauki matakin ne a wani taron gaggawa da suka gudanar ranar Laraba.

NLC ta ce zanga-zangar za ta zama gargaɗi ga hukumomi kan yunkurin kakabawa mutane ƙarin kuɗin kiran waya a ƙasa kuma da albashi mafi ƙanƙanta bai wuce naira 70,000 ba, ga kuma ƙarin farashin mai da na abinci da lantarki da kuma ƙaruwar hauhawarar farashi.

ƙungiyar ta buƙaci rassanta na jihohi da su fara shirya mambobinsu domin shiga zanga-zangar ta ƙasa baki-ɗaya, inda ya yi kira ga ƙungiyoyin fararen hula da su ma su fito.

Ta kuma yi kira ga ma’aikata da kuma ɗaukacin ‘yan Nijeriya da su tsaya kai da fata wajen yin watsi da wannan tsari da kuma waɗanda ba su alheri gare su.

ƙungiyar ƙwadagon ta kira yi gwamnatin tarayya da NCC da hukumar majalisar tarayya da su zauna don tattaunawa da masu ruwa tsaki domin sake duba wannan ƙari a daidai lokacin da ‘yan ƙasar ke fama da matsin tattalin arziki.

By ukarofi