Yadda masu ɗibar fetur daga tankar da ta faɗi suka kai wa jami’an kashe gobara hari

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

Masu ɗibar man fetur daga wata tankar mai da ta faɗi sun kai wa jami’an kashe gobara da ke hana su farmaki.

Bayan faɗuwar tankar a cikin dare man cikinta ya fara tsiyaya, inda motar ta kama da wuta a kan babbar hanyar Ogbomosho zuwa Ilorin a ranar Laraba.

Faɗuwar motar ke da wuya wasu mazauna yankin Kasuwar Sabo, da ke Orile Igbon, suka fara tururuwar zuwa ɗibar man.

Jami’an kashe gobara da suka zo aikin ceto bayan aukuwar hatsarin sun nemi hana mutanen zuwa ɗuban, amma sai mutanen suka bijire suma far musu.

By ukarofi