Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Yayin da damina ke ƙaratowa, hasashen Hukumar Kula da Harkokin Ruwa ta Nijeriya (NIHSA) da Hukumar Hasashen Yanayi ta Nijeriya (NiMet) sun nuna cewa za a fuskanci ruwan sama mai ƙarfi a jihohi 33 da fiye da yankuna 14,000 a faɗin ƙasar nan, ciki har da Jihar Jigawa, Hukumar Wayar da Kai ta ƙasa (NOA) a jihar ta sanar da fara gangamin wayar da kai domin rage illar ambaliya da kuma shirye-shiryen ko-ta-kwana.
Daraktan Hukumar NOA na Jihar Jigawa, Ahmad Tijjani Ibrahim, ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai da aka gudanar a Dutse domin ƙaddamar da shirin wayar da kan jama’a.
A cewarsa, duk da cewa ambaliya lamari ne na ɗabi’a, ayyukan ɗan Adam sun ƙara tsananta illar ambaliyar ruwa a yankuna da dama.
Ya bayyana cewa, matsaloli irin su rashin ingantattun magudanan ruwa, zubar da shara ba bisa ƙa’ida ba cikin hanyoyin ruwa, gine-gine a kan hanyoyin ruwa da kuma yawaitar sare itatuwa sun taimaka matuƙa wajen yawaitar ambaliya a al’ummomi daban-daban.
Daraktan ya ce, hukumar za ta tura Jami’an Wayar da Kai na Al’umma zuwa ƙananan hukumomi 27 na jihar domin ilmantar da jama’a kan hanyoyin kauce wa ambaliya da yadda za su ɗauki matakan gaggawa idan lamarin ya faru.
Ya ƙara da cewa, hukumar za ta ci gaba da aiki tare da hukumomin da abin ya shafa domin tabbatar da isar da sahihan bayanai cikin lokaci kan hanyoyin kariya daga ambaliya da matakan ceto.
“Muna kira ga jama’a da su ƙara kula da tsaftar muhalli tare da rungumar shuka itatuwa domin rage haɗarin ambaliya,” inji Ibrahim.
A wani ɓangare kuma, Daraktan na NOA ya yi magana kan mataki na uku na ci gaba da rajistar masu kaɗa ƙuri’a wanda ya fara ranar 11 ga watan Mayu.
Ya buƙaci duk ‘yan ƙasar da suka kai shekaru 18 da haihuwa da su yi anfani da damar wajen yin rajista domin samun damar kaɗa ƙuri’a a zaɓe mai zuwa.
Ibrahim ya tabbatar da cewa jami’an wayar da kai na hukumar za su yi aiki tare da shugabannin al’umma da sauran masu ruwa da tsaki domin ƙarfafa gwiwar jama’a su fito domin yin rajista.
“Hukumar Wayar da Kai ta ƙasa tana kira ga duk waɗanda suka cancanta su yi anfani da wannan dama domin yin rajista tare da karɓar Katin Zaɓe na Dindindin (PɓC),” inji shi.
Ya ƙara da cewa, hukumar za ta ci gaba da haɗa kai da hukumomin da abin ya shafa domin rage yawaitar ambaliya a Jihar Jigawa.
