Obi ya samu tikitin takarar shugaban ƙasa na NDC

Spread the love

Daga USMAN KAROFI

Ɗan siyasa kuma tsohon gwamnan Jihar Anambra, Peter Obi, ya zama ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Nigeria Democratic Congress (NDC) a zaɓen shekarar 2027. Yayin karɓar tutar takarar a Abuja, Obi ya bayyana cewa Najeriya ba ta da wani dalili na kasancewa cikin ƙasashen da suka fi fama da yunwa a duniya, yana mai jaddada cewa “Sabuwar Najeriya mai kyau mai yuwa ce.”

Obi ya yi alƙawarin farfaɗo da tattalin arzikin ƙasa, samar da ayyukan yi, magance matsalar tsaro da kuma bunƙasa harkokin noma domin kawo ƙarshen yunwa. Ya ce idan aka zaɓe shi, gwamnatinsa za ta ƙara samar da wutar lantarki da aƙalla megawatt 10,000 cikin shekaru huɗu, yana mai bayyana cewa ƙarancin wutar lantarki na daga cikin manyan matsalolin da ke hana ci gaban tattalin arzikin Najeriya.

Dangane da tsaro, Obi ya ce zai yi amfani da fasahar zamani da bayanan sirri wajen yaƙi da matsalar rashin tsaro, tare da magance tushen matsalolin da suka haɗa da talauci da rashin aikin yi. Haka kuma ya yi alƙawarin ƙara kasafin kuɗin kiwon lafiya, faɗaɗa tsarin inshorar lafiya da tabbatar da cewa kowace daga cikin mazaɓu 8,809 na ƙasar nan tana da cibiyar lafiya ta matakin farko mai aiki yadda ya kamata.

A ɓangaren ilimi da tattalin arziki, Obi ya ce zai ƙara zuba jari a makarantu, horas da malamai da bunƙasa ilimin sana’o’i da fasaha. Ya kuma yi alƙawarin tallafa wa ƙananan da matsakaitan masana’antu ta hanyar sauƙaƙa haraji da samar da rance mai rahusa. Tun da farko, jagoran jam’iyyar NDC, Seriake Dickson, ya miƙa wa Obi tutar jam’iyyar, yayin da shugaban jam’iyyar, Moses Cleopas, ya bayyana cewa NDC na da cikakken shiri na bai wa ‘yan Najeriya wata sabuwar mafita a zaɓen 2027.

By ukarofi

Leave a Reply