Patama Leeswadtrakul: Gasar Olympics ta lokacin hunturu ta Beijing ta gabatar da abubuwan gado masu daraja

Daga CMG HAUSA

Shugabar kwamitin kula da harkokin al’adu da abubuwan gado na kwamitin shirya gasar Olympics na duniya, kana, mambar kwamitin gasar Olympics na ƙasa da ƙasa na ƙasar Thailand, Patama Leeswadtrakul ta yaba matuƙa da gasar Olympics ta lokacin hunturu da gasar Olympics ta lokacin hunturu ta nakasassu ta birnin Beijing. Tana mai cewa, ƙasar Sin ta nuna wa ƙasashen duniya ƙwarewarta wajen aiwatar da babbar gasa ta ƙasa da ƙasa, inda ta bar dimbin abubuwan gado masu daraja a fannin wasannin Olympics.

Ta ce, gasar Olympics ta lokacin hunturu ta nakasassu ta Beijing ta cimma nasarar sa ƙaimi ga masu buƙata ta musamman a ƙasashen duniya da su fara wasannin motsa jiki. Ta ce ƙasar Sin tana da ƙwarewa matuƙa wajen gudanar da irin wannan babbar gasa ta duniya, ta kuma mai da hankali kan gudanar da gasar ta hanyar kare muhalli.

Bugu da ƙari, ta ce an daidaita wuraren wasannin motsa jiki na gasar Olympics da dama zuwa wuraren wasannin motsa jiki na gasar Olympics ta lokacin hunturu ta nakasassu, bisa buƙatun ‘yan wasan motsa jiki masu buƙata ta musamman, lamarin da ya nuna kulawar Sin kan masu buƙata ta musamman sosai. (Mai

Fassarawa: Maryam Yang