Daga CMG HAUSA
Kamfanin samar da suga na ƙasar Habasha, ESC, ta bayyana cewa, sabuwar masana’tarta na samar da Suga ta Tana Bales No.1 sugar factory, ta fara aiki.
Cikin wata sanarwa da ya fitar a jiya, kamfanin ESC ya ce masana’atar sugan, wadda kamfanin gine-gine na CAMCE na ƙasar Sin ya gina, ta fara aikin samar da Suga a ranar Alhamis, bayan shafe watanni tana gudanar da shirye-shirye.
An fara aikin ginin masana’atar sugar dake yankin Amhara na arewacin ƙasar ta gabashin Afrika ne a shekarar 2012, inda aka tsara kammalawa cikin watanni 18. Sai dai, aikin ginin bai tafi kamar yadda aka tsara ba. inda zuwa ƙarshen shekarar 2017, kaso 60 na aikin kaɗai aka kammala.
CAMCE, wanda mallakin kamfanin samar da injinan masana’atu na ƙasar Sin ne, ya karɓi aikin ginin ne a watan Satumban 2019.
ESC ya bayyana cewa, ana sa ran masana’atar zata samar da suga metric ton 20,000 a ƙashen shekarar kuɗi ta ƙasar da ake ciki ta 2021/2022, wadda zata zo ƙarshe a ranar 7 ga watan Yuli.
Fassarawa: Fa’iza Mustapha