Babban Taron APC: Za mu ba wa maraɗa kunya, inji Buhari

Daga BAKURA MUHAMMAD a Bauchi

Shugaban Ƙasa, Muhammadu Buhari ya bayyana cewar, jam’iyyar APC tana da kuzarin kawo maslaha dangane da bambance-bambance dake akwai a tsakanin ‘ya’yan ta kan lamuran zaɓen shugabannin ta da za a gudanar nan ba da jimawa ba.

Shugaba Buhari, wanda ya yi adabon barin Abuja zuwa birnin Landan ta ƙasar Biritaniya a ranar Lahadi da ta gabata dangane da abinda ya kira, ‘Tuntuɓar kiwon lafiya’, ya ce la’akari da tanade-tanaden tsarin mulkin ƙasa, mataimakin shugaban ƙasa, Yemi Osinbajo zai riƙe madafun mulki yayin da ba ya nan.

Jam’iyyar APC dai, ta dulmuya cikin rakacaniya ta cikin gida dangane da jirga muƙaman siyasa zuwa shiyya-shiyya, lamarin da yake ci wa jam’iyyar tuwo a ƙwarya.

Rahotanni sun bayyana cewar, Shugaba Buhari ya nuna goyon bayansa ga Sanata Abdullahi Adamu, tsohon gwamnan jihar Nasarawa a matsayin shawartaccen shugaban jam’iyyar na ƙasa, illa dai wasu ‘yan takara na wannan kujera an yi zargin sun bujure wa wannan tsari, da suka bayyana da ƙarfa-ƙarfa da ya yi banbaraƙwai da tsarin dimokraɗiyya.

Amma duk da yawan rigingimun cikin gida na jam’iyyar, Shugaba Buhari ya ce babu wani abin damuwa a ciki, domin jam’iyyar tana da duk yadda za ta iya na sarrafa komai cikin hayyaci.

Da yake amsa wata tambayar manema labarai kafin ya taka jirgin sa zuwa Landan, akan me zai shaida wa ‘yan Nijeriya waɗanda suke da shakkar yadda jam’iyyar APC za ta gudanar da taron ta na zaɓen shugabanni cikin nasara, sai shugaban ƙasa ya ce, “eh, a jira a gani.

“Yaya muka kasance a matsayin mu na jam’iyya, muka ƙwace mulki daga wajen gwamnati mai ci wacce take kan karaga shekara da shekaru? Don haka, muna da yadda za mu yi, kuma komai zai daidaita.”

Dangane da giɓin da za a samu sakamakon baya cikin ƙasa, sai ya ce, “eh, ai bani kaɗai zan gudanar da komai da komai ba, mataimakin shugaban ƙasa yana nan. Bisa tanade-tanaden dake cikin kundin tsarin mulkin ƙasar nan, idan bani nan, shi zai riƙe ragamar mulki. Kuma ga Sakataren Gwamnatin Tarayya, ga kuma shugaban ma’aikata na fadar shugaban ƙasa, saboda haka babu wata matsala.”

Shugaban Ƙasa Buhari dai, ya miƙe ƙafa zuwa Landan domin a duba lafiyar sa, ana kuma sa ran dawowar sa cikin sati biyu.

Shugaban Ƙasa dai, satin da ya gabata, ya je Nairobi, babbar birnin ƙasar Kenya domin ya martaba gayyatar da wancan shugaba, Uhuru Kenyatta ya yi masa na cikar ƙasar shekaru hamsin da aiwatar da wani shirin inganta yanayin ƙasa na Majalisar Ɗinkin Duniya mai taken ‘UNEP@50’.

A wata sanarwa da mai bai wa shugaban ƙasa shawara na musamman akan kafofin watsa labarai da faɗakarwa, Cif Femi Adesina ya fitar, ta ce Shugaba Buhari daga Kenya zai zarce zuwa Landan, inda za a duba lafiyar sa, kuma tafiyar za ta ɗauki sati biyu.