PDP ta buƙaci tsohon gwamna Fayose da ya fice daga jam’iyyar

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

Jam’iyyar PDP a Jihar Ekiti ta buƙaci tsohon gwamnan jihar, Ayodele Fayose, da ya fice daga jam’iyyar bayan sukar da ya yi mata.

Shugaban Kwamitin Riƙon ƙwarya na PDP a jihar, Dare Adeleke, ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar, inda ya ce Fayose ya ci amanar jam’iyya kuma yana ci gaba da ɓata sunanta duk da cewa yana iƙirarin zama cikakken mamba.

Fayose, a wata hira da aka yi da shi a talabijin, ya ce PDP ta lalace, ruhi da tunaninta sun tafi, yana mai cewa jam’iyyar za ta zo ta huɗu a zaɓen 2027. Ya zargi shugabannin jam’iyyar da raina gudunmawarsa duk da sadaukarwar da ya yi.

Sai dai Adeleke ya mayar da martani, yana tambayar dalilin da ya sa Fayose ke ci gaba da zama a jam’iyyar da ya kira “gawa” da “jam’iyyar da ta mutu”.

Ya ce dukkan shugabannin PDP na kananan hukumomi a jihar sun nesanta kansu da Fayose tare da sukar halayensa. 

Adeleke ya bayyana cewa Fayose bai da tasiri a siyasa kamar yadda yake iƙirari, inda ya jaddada cewa PDP za ta ci zaɓen gwamna a 2026 da ‘yan jam’iyya na gaskiya.

Adeleke ya kammala da cewa PDP a Ekiti tana da karfi kuma ba za ta bar wadanda ke bata mata suna su hana ta ci gaba ba.

By ukarofi