

Daga HABU ƊAN SARKI a Jos
Shugaban Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Filato (PLASIEC), Planji Chishak ya sanar da cewa Jam’iyyar PDP ce ta lashe zaɓe a dukkan Ƙananan Hukumomi 17 na jihar, a zaɓen da aka gudanar a ranar Laraba, 9 ga watan Oktoba, 2024.
Da farko a daren Alhamis, sakamakon ƙananan hukumomi 10 aka fara fitarwa inda daga bisani aka fitar da ƙarin wasu biyar.
Gwamnatin jihar da shugabannin PDP na jihar suka shirya gagarumin taro cikin daren don murnar lashe zaɓen da suka yi tare da rantsar da sabbin shugabannin 15, waɗanda suka karɓi takardun shaidar samun nasarar su daga PLASIEC.
A ranar Juma’a ne aka sanar da ragowar ƙananan hukumomi biyun da suka rage waɗanda sune Pankshin da Langtang ta Arewa inda a nan ma PDP ce ta yi nasara.
Daga bisani, Gwamna Caleb Mutfwang ya rantsar da su bayan sun karɓi takardun shaidar cin nasara.
Sai dai akwai wasu cibiyoyin zaɓe 7 da za a sake zaɓe nan gaba a ƙananan hukumomin Bassa, Mangu, da Jos ta Gabas, waɗanda aka soke zaɓensu bisa dalilai na rikici da rashin cikakkun takardun zaɓe.
Kakakin jam’iyyar adawa ta APC, Shittu Bamaiyi, ya zargi PDP da PLASIEC da shirya maguɗin zaɓe ta ɓarauniyar hanya, inda aka riƙa bayar da takardun ƙuri’u da ba su cika ba.
A wata cibiyar zaɓen ma waɗanda aka bayar ba su fi rabin mutanen da suka yi rijista a wajen ba.
Saidai, a jawabinsa na taya murna ga sabbin kantomomin, Gwamna Mutfwang ya yaba wa PLASIEC game da ƙoƙarin da ta yi wajen shirya zaɓen cikin tsari da inganci fiye da zaɓukan da aka yi a baya.
Sannan ya yi kira ga zaɓaɓɓun kantomomin su tabbatar sun gudanar da ayyukan da za su raya yankunansu ta yadda jama’a za su amfana daga mulkin dimokraɗiyya tare da samun sauƙin rayuwa.
